Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da daliban makarantar kwana ta Kankara dake Katsina bayan kubutar da su daga hannun ‘yan bindigar da suka sace su. Shugaban ya gana da daliban ne a fadar gwamnatin Katsina kwana guda bayan ceto ɗalibansu sama da 340.
An kubutar da daliban ne, wanda yawancinsu yara ne kanana a jiya Alhamis bayan shafe kusan tsawon mako daya a daji a hannun masu garkuwa.
Buhari ya jinjinawa gwamnatin Katsina da kuma sauran wadanda suka taimaka aka kubutar da daliban. Shugaban ya fara yin jawabin ne da yin kira ga daliban su saurare shi kuma su fahimce shi.