Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Gana Da Gwamnonin Jam’iyyar APC Kan Rikicin Jam’iyyar

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi wata ganawa da wasu gwamnonin Jam’iyyar APC dangane da rigingimun da suke addaban Jam’iyyar.

Ganawar ta su wacce suka yi a cikin fadar shugaban kasa da ke Abuja, wani yunkuri ne na ganin sun warware rikicin Jam’iyyar da a yanzun haka ya dabaibaye Jam’iyyar ta APC.
Gwamnonin wadanda suke a karkashin jagorancin shugaban kungiyar gwamnonin Jam’iyyar ma’abota kawo sauyi, Gwamna Atiku Bagudu, na Jihar Kebbi.
Sauran a wajen ganawar har zuwa lokacin hada wannan rahoton sun hada da, Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong; da takwararsa na Jihar Jigawa, Abubakar Badaru.
Da suke magana da manema labarai na fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja, a bayan ganawar na su, gwamnonin sun ce sun gabatar wa da shugaba Buhari matsayinsu a kan rikicin shugabancin da ya addabi Jam’iyyar.
Sun kuma nuna goyon bayan shugaban kasan wajen shirya duk wasu taruka da kowane bangare domin kawo matakin karshe na rikicin da ke cin Jam’iyyar a halin yanzun.
Bagudu ya ce shugaba Buhari ya ba su tabbacin daukan duk wasu matakan da suka dace wajen ganin an dawo da zaman lumana a cikin Jam’iyyar.
Ya kara da cewa, duk da shugaban kasan ya nu na ba zai tilasta ikonsa a kan shugabancin Jam’iyyar ba, amma ya ce yana cikin damuwa da abubuwan da suke faruwa a cikin Jam’iyyar kuma a shirye yake ya yi duk abin da ya dace domin lafar da kurar da ta turnuke.
“Daman babban dalilin kai ziyarar namu shi ne a matsayinsa na shugaba mu sanar da shi tare da neman sa bakinsa a kan abubuwan da suke faruwa a cikin Jam’iyyarmu. Shugaban kasan ya saurare mu sosai, ya kuma ba mu tabbacin nan ba da jimawa ba za a warware dukkanin matsalolin.
“Bari na sake yin gargadi da cewa, Jam’iyya fa ba ta iya kasancewa ba tare da ‘yar hayaniya ba. tilas ne a rika samun ‘yan maganganu irin wannan da muke Magana a kai a halin yanzun, a irin haka, bangarorin Jam’iyya ne ya kamata su zauna tare da shugaban kasa domin warware duk wata matsala da ta taso.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: