Shugaban kasa Muhammadu Buhari yaja kunnen hukumonin dake tarawa gwamnatin tarayya da kudaden aden shiga inda ya ce idan suka gagara kawo abinda aka shata masu za su fuskanci hukunci matsananci .
Buhari yayi gargadin ne a lokacin da yake yin jawabi ga ‘yan Nijeriya a kan bikin zagayowar ranar cikar kasar nan shekaru 59 da samun ‘yancin kai.
Hukumomin dai sune, Hukumar hana fasa kwauri da mai tara haraji wato FIRS da DPR da dai sauransu.
A cewar shugaba Muhammadu Buhari, kokarin da gwamntin maici take kan yi na samar da ci gaba, kwaliyya tana buyan kudin sabulu a fannin tattalin arzikin kasar nan.
Ya ci gaba da cewa, ma’aikatun guda biyu su ne ke da alhakin kula da duk wani shige da ficen kudaden ga gwamnatin tarayya, musamman ga masu kananan sana’o’i.
Shugaba Buhari ya ce, a don haka ya zama wajibi mu sanya ido ga hukumomin dake samarwa da Nijeriya kudaden shiga, ta yadda zai kasance komi na tafiya yadda ya kamata, inda shugaban ya kuma yi nuni da cewa, sai dai kuma idan muka samu akasin hakan daga wata hukuma to hakika za ta fuskanci hukunci.
A cewar Buhari, burin dai a nan shi ne ya kasance ko wace hukuma ta iya kawo abinda aka yanke mata domin a matsayin kudaden shiga da ya kamata ta kawo.
A karshe Shugaban kasar ya kuma sanar da cewa, ma’aikatar kudin da kasafin kasa na musamman ta fitar da naira biliyan N600 domin yin wasu manyan ayyukan raya kasa cikin watanni uku.