Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Gaza A Gwamnatinsa, In ji Baba-Ahmed

Published

on

Ma’assasin Jami’ar da zai koma dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Sanata Datti Baba-Ahmed ya shaida cewar shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya gaza wajen gudanar da gwamnati nagartatta.

Sanata Datti ya shaida hakan a jiya Juma’a a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke Abuja a yayin da ke gabatar da bukatarsa na tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a zaben da ke tafe na 2019.

Tsohon dan majalisar ya shaida cewar Buhari ya yi tutiyar yaki da cin hanci da rashawa amma kuma cin hanci da amsar rashawa na ci gaba da hauhuwa a gwamnatinsa.

Ya ke cewa; “Zancen yaki da cin hanci da rashawa zancen karya ne kawai. Ina son rayuwata sannan kuma ina matukar son Nijeriya. Ta yaya za ku tattara kudaden albashin mutane ku zo ku ce kuna yaki da cin hanci da rashawa? Cin hanci da rashwa ta karu ne ma a wajen gwamnoni da rassan gwamnatoci.

“Shi (Buhari) ya shaida wa taron manema labaru na kasa da kasa yana mai musanta zancen bai wa ‘yan uwansa kwantiragi, amma kuma kisan da shekar da jinin mutane a kasar na ci gaba da wakanuwa kulliyaumin.

“Gabanin APC ta amshi mulkin kasar nan, an samu raguwar aikace-aikacen ta’addanci,” In ji dan takarar.

Ya kara da cewa; “Matukar APC ta sake dawowa mulki a karo na biyu 2019, faracin dala sai ta kai N700. Matukar APC ta sake dawowa a 2019 za a tsunduma cikin mawuyacin hali a wannan kasar, ina mai shaida cewar ya kamata mu hanzarta ceto Nijeriya daga masu neman hallakata,” In ji Datti.

Datti Baba Ahmed ya ci gaba da jawabinsa da cewa; “Cikin tsautsayi APC ta dale kan karagar mulkin kasar nan, amma a sakamakon rashin tsari mai kyau tun daga Gundumomi sai ga shi Nijeriya tana halin da take ciki,” Ya kara shaidawa.

Dakta Baba-Ahmed ya shaida cewar ya amince ya nemi tikitin jam’iyyar PDP domin tsayawa takarar koda kuwa jam’iyyar ba za ta bashi wannan tikiti ba.

Daga bisani ya nemi kwamitin (NWC) na jam’iyyar da su yi aikinsu bisa gaskiya da rikon amana domin kowani dan takara ya samu shiga a dama da shi domin fid da nagartaccen dan takara a jam’iyyar.

Da yake tasa jawabin, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus ya bukaci shugaban Nijeriya Muhamamdu Buhari da ya kawo karshen kashe-kashen rayuka da ake yawan samu a fadin kasar nan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: