Buhari Ya Gaza Kawo Batun Bunkasa Tattalin Arzikin Nijeriya A Ganawarsu Da Trump –PDP

Daga Umar A Humkuyi

 

Jam’iyyar PDP, ta yi tir da rashin katabus din da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a tattaunawar da suka yi da Shugaban Amurka, Donald Trump, a fadar gwamnatin Amurkan ranar Litinin, Jam’iyyar ta kwatanta rashin katabus din Shugaba Buharin da cewa abin kunya ne, domin ya kasa ya bayyana hanyoyin da ya kamata Amurkan ta taimaka wa Nijeriya.

Jam’iyyar ta fadi hakan ne ranar Litinin a Abuja, ta hannun Kakakin ta, Kola Ologbondiyan.

Jam’iyyar adawan ta ce,abin kunya ne yadda Shugaban Nijeriyan duk ya dmauce sa’ilin tattaunawar, ya kasa yin maganan dalilin koma bayan da aka samu wajen danyan man da Amurkan kan saya daga Nijeriyan, wanda shi ne kashin bayan tattalin arzikinmu.

“’Yan Nijeriya sun sha mamakin yadda Shugaba Buhari ya kasa tallata danyan man namu ga takwarar na shi na Amurka, hatta a lokacin tambayoyi da amsan da suka yi da manema labarai, inda har satan amsa aka ba shi, amma ya zubar da wannan daman.

“Hakanan, Shugaba Buhari, ya kasa bayar da amsa ga Donald Trump, kan matsayin na Amurka da ta ki zuba wani jarin kirki a Nijeriya, bisa dalilin gurbacewan tattalin arzikin Nijeriyan, wanda hakan ke dada gaskata fadar da muke cewa, APC, din tana tafiya ne kan tattalin arzikin da ta rusa.

“Babban abin bakin cikin ma shi ne, tona asirin da Shugaba Donald Trump ya yi na cewa, gwamnatin ta Amurka tana tallafawa Nijeriya da dala bilyan 1 a duk shekara, inda Shugaba Buhari, a na shi bayanin ya ce, Nijeriya ta karbi gudummawar dala milyan 500 daga hannun Amurkan a shekarar da ta gabata.

“Mun yi tsammanin Shugaba Buhari, a matsayin sa na jagoran yaki da cin hanci da rashawa a Afrika, zai yi gaggawan amsa wa Shugaban Amurkan kan inda sauran dala milyan 500 din suka makale.

“Ba abu ne da za a yafe ba, yadda Shugaba Buhari ya gaza bayar da amsan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a kullum ta hanyar zubar da Jinainai da kashe-kashen rashin Imani ga ‘yan Nijeriya, wanda Shugaba Trump, ya bayyana da cewa,abin tashin hankali ne. sai kawai Shugaba Buhari, ya takaitu ga abin da ke rubuce a cikin takardar hannun shi, wacce ba ta da bayanin wadannan lamurran. Hakan ya nu na gwamnatin ta Amurka ta kama gwamnatin ta Shugaba Buhari, da laifin kasa samar da tsaron dukiyoyi da rayukan ‘yan Nijeriya.

“Bakidaya dai, ziyarar ta iya samar da hoto ne kawai na Shugaba Buhari a fadar gwamnatin ta Amurka, inda Shugaba Donald Trump, ya tallata kasarsa ga jagorar kasashen na bakaken fata.

 

Exit mobile version