A ranar Talata ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya godewa ‘yan Nijeriya bisa hakuri da matsalolin tattalin arzikin da suke fuskanta, ya kuma bukaci su da su ci gaba da hakuri da matsalolin da kasar nan take fuskanta. A cewar kalamun mai bai wa shugaban kasa shawara ta fannin yada labarai, Femi Adesina ya bayyana Buhari ya fadi haka ne wajen taron shirin fadada gas din kasa wanda ya gudana a fadarsa da ke Abuja.
Bayanin mai taken ‘Buhari ya godewa ‘yan Nijeriya bisa hakuri da matsalolin tattalin arziki, ya kuma bukace su da su dunga amfani da gas a madadin man fetur’.
Adesina ya bayyana cewa, shugaban kasa ya bayyana cewa, “bari in nuna godiya ta ga ‘yan Nijeriya bisa hakurinsu da kungiyar kwadugo, bisa hakuri da matsalolin tattalin arziki wanda duniya ta fuskanta.”
Buhari ya bukaci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da amfani da gas maimakon man fetur.Ya kara da cewa, albarkatun iskar gas wanda Nijeriya take alfahari da shi tare da amfani da shi wajen bunkasa ababen more rayuwa a nan cikin gida Nijeriya.