Rabiu Ali Indabawa" />

Buhari Ya Halarci Taro Da Sarkin Urdu Da Narenda Modi Na Inidya

Daga isarsa kasar Saudiyya, Shu gaba Muhammadu Buhari ya fara halartan tarruruka a birnin Riyadh inda ya tattauna abubuwan da Nijeriya ke bukata na sa hannun jari da kasuwanci. Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Buhari ya gana da wasu shugabannin kasashen duniya a ranar Talata a Otal na Ritz Carlton na kasar. Jawabin ya ce: “Gabanin ganawar da zai yi da shugabannin kasashen Afrika, shugaba Buhari a ranar Talata ya halarci taro da sarkin Urdu, Abdullah na biyu, da firam ministan Indiya, Narenda Modi.

Shugaban kasar zai halarci taro ranar Laraba inda shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou; shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta da shugaban kasar Congo-Brazzabille, Denis Sassou-Nguesso domin tattauna kan cigaba nahiyar Afrika.”

 

 

Exit mobile version