Sani Hamisu" />

Buhari Ya Jajenta Harin Da Aka Kai Wa Kiristoci A Kasar Sirilanka

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi bakin ciki tare da jajenta abinda ya faru a Sirilanka, sakamakon wani mummunan hari da a ka kai majami’a a jiya Lahadi, wanda hakan ya jawo mutane da dama su ka rasa rayukansu, wasu kuma su ka tsira da raunuka a jikinsu.
Shugaban ya sanar hakan ne ta hanyar mai magana da yawunsa a kafar sadarwa, Malam Garba Shehu, a Abuja ranar Lahadi.
Buhari ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda su ka mutu a lokacin, kana ya mika jajantawarsa ga wadanda su ka tsira da rauni.
“Mu na fama da ’yan ta’adda a fadin duniya, wadanda su ke aiwatar da mummunan aikin kai hare-hare kuma su kashe mutane, “in ji shugaban.
Ya bukaci hukumomin kasar da su gudanar da bincike akan wannan lamarin sannan su dauki matakin da ya da ce akan masu abun.

Exit mobile version