Buhari Ya Je Sakkwato Ta’aziyyar Marigayi Shehu Shagari

A jiya be shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nufi garin Sakkwato don yin ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban kasa Shehu Aliyu Shagari, wanda ya rasu a ranar 28/12/2018 a babban asibitin Abuja.

Shugaba Buhari tare da ‘yan rakiyarsa sun sauka ne filin jirgin sama na Sultan Abubakar III inda gwamnonin jihohin Sakkwato da Kebbi, Aminu Waziri Tambuwal da Atiku Bagudu suka tarbe shi.

Cikin wadanda suka tarbi shugaban kasar sun kuma hada da shugaban kungiyar sanatocin Arewa, Sanata, Aliyu Magatakarda Wamakko da tsohon gwamnan jihar Attahiru Dalhatu Bafarawa, da tsohon Minmistan Sifiri, Yusuf Suleiman, da kuma dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC, Ahmed Aliyu Sokoto, da sauran ‘yan jam’iyyar da dukan sassan jihar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya zarce ne kai tsaye zuwa gidan tsohon shugaban kasar Shehu Aliyu Shagari, dake layin Sama da ke a cikin garin na Sakkwato inda Alhaji Bala Shagari ya tarbe shi.

Bala Shagari ne babban dan marigayyi tsohon shugaban kasar kuma shi ne Marafan Shagari. Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal, ne ya karanta sakon shugaban kasa, daga baya kuma shugaban kasar ya yi alkawarin karrama marigayyin.

Sakon ta’aziyyar ya kuma ci gaba da cewa,

“Na samu sakon rasuwar Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, tsohoin shugaban kasar tarayyar Nijeriya cikin alhini.

“Labarin rasuwar abu ne da ya ratsa dukkn sassan kasar nan duk kuwa da banbance banbance da muke da shi a kasar nan. Marigayyi Alhaji Shagari na daya daga cikin mazan jiya da suka hada wannan zamanin da zamanin gwamnatin Alhaji Abubakar Tafawa Balewa, shi ne kuma dan Nijeriya na farko da ya zama shugaban kasa mai cikakke iko a Nijeriya.

“Ina mai mika ta’aziyya ta ga dukkan ‘yan uwa da jama’ar jihar Sakkwato da kuma gwamnatin jihar a bisa rashin wannnan dan Nijeriya mai kishin kasa.

“Gwamnatin tarayya zata kafa wani cibiya don ci gaba da tunawa da tsohon Shugagan Kasan, da fatan Allah Ya jikansa.”

Da yake jawabi amadadin iyalan marigayyin, Bala Shagari ya gode wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a bisa wannnan ziyarar ta’aziyyar.

Exit mobile version