Buhari Ya Kaddamar Da Shiri Don Shigar Da Matasa 774,000 Harkar Noma

Daga Khalid Idris Doya

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekaran jiya ne ya kaddamar da wani shirin noma na kasa domin matasa wanda ke karkashin hukumar bunkasa noma ta kasa (NALDA) da zai bada dama ga matasa dubu-dubu a daukacin kananan hukumomi 774 a fadin kasar nan don su shiga harkar noma a dama da su.

Kaddamar da shirin wanda ya gudana a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Buharin ya nemi hukumomin da lamarin noma ya shafa da su ke tabbatar da shirgar da matasa cikin tsare-tsarensu domin bunkasa harkokin noma na zamani a fadin kasar nan.

A cewar sanarwar manema labarai da Kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya fitar, shugaban kasa ya tabbatar wa dukkanin bangarorin da suke da sha’awar shiga tsarin da cewa suna da damar yin hakan domin kuwa an samar da tsari mai nagarta da zai taimaka wa matasa matuka.

Buhari ya ce har zuwa yanzu noma na daga bangare na gaba-gaba da ke jagorantar tattalin arzikin Nijeriya, yana mai misalta noma a matsayin babban hanyar da ya fi bada gudunmawa wa Gross Demostic Product (GDP).

Sanarwar ta Adesina ta ce, Buhari na cewa, “Za mu kara kaimi domin fadada sashin noma, zamanantarwa da kuma tabbatar da kawo sauyi ga sha’anin noma, wanda shine mafi kima ga arzikinmu.

“Na bada umurnin dukkanin gonakan NALDA da aka wofintar da su a farfado da su gami da baiwa matasa maza da mata domin su tsunduma sha’anin noma. Wannan gwamnatin za ta cimma manufar inganta noma ta wannan shirin, kuma ina da tabbacin da kwarin guiwar cewa a karkashina Nijeriya za ta samu wadatar abinci da bunkasar abinci mai kyawu da za mu ci. A cikin shekaru za mu iya fitar da abincin da muke nomawa ga kasashen waje domin samun kudaden shiga.”

“A matsayina na mai sha’awar noma wanda ni kaina manomi ne, na bada umurnin ake sanya ido kan hukumar NALDA kai tsaye daga fadar shugaban kasa domin tabbatar da lamuran suna tafiya yadda ake so.

“Sannan, na kuma bukaci ma’aikatar gona ta tarayya da gwamnatocin jihohi da su bada cikakken goyon baya ga dukkanin aikace-aikacen NALDA. Tare da nasarar shirin Anchor Barrowers wanda babban bankin CBN ya jagoranta tare da sabbin shirye-shiryen kan noman auduga, dabino da koko, nan da wasu ‘yan shekaru masu zuwa za mu ga canji sosai kan sha’anin nomanmu bisa kokarin da ake sanyawa,” ya ce.

Shugaban kasar ya bada tabbacin amincewa da dukkanin ababen bukata ga shirin NALDA domin tabbatar da tsare-tsaren da aka fitar sun tafi yadda ake so.

Ya kalubananci babban sakataren NALDA, Mista Paul Ikonne, tare da ‘yan tawagarsa wajen ganin an samu nasarar shirin tare da neman su shiga lunguna da sako domin ganin matasa sun shiga shirin tare da amfana da shi sosai.

“An fada min cewa, zuwa yanzu, magidanta 4,333 sun ci gajiyar wannan shirin, ana tsammanin wasu karin daidaiku da magidanta za su amfana da wannan shirin da aka fara.

“Yanzu na kaddamar da wannan shirin domin matasa su tsunduma harkar noma. Ina tsammanin matasa wadanda suka kammala karatu da wadanda ba su kammala karatu ba su shiga cikin shirin, dukka wannan matakan na daga cikin yunkurin gwamnati na rage yawan marasa aikin yi da kuma tabbatar da samar da kudaden shiga wa kasar nan domin kyautata tattalin arzikin Nijeriya,” Inji Buhari.

Sanarwar ta ce, shugaban majalisar dattawan Nijeriya Sanata Ahmad Lawan ya jinjina wa shugaban kasa a bisa tabbatar da wannan shirin, tare da sa’ayin Buhari kan farfado da harkokin noma a kasar nan.

A cewar Lawan irin wannan shirye-shiryen za su bada dama a riski al’umma tun daga tushe domin ganin su ma sun mori gwamnati.

Sanarwar ta ce, wannan tsarin zai bada damar rage kaifin talauci da fatara da ke tsakanin jama’an Nijeriya.

Babban sakataren NALDA, Mista Paul Ikonne ya sha alwashin yin duk mai yiyuwa domin tabbata da nasarar shirin.

“Manufarmu shine a samar da manoma 1,000 a kowace karamar hukuma 774, hakan zai bada damar samar wa matasa 774,000 ayyukan yi, kai tsaye kowani shekara,” Inji shi.

Adesina, a sakon fatan alkairi da suka gabatar a madadin matasa manoma, Fatima Usman Musa da jakadan kasar Denmark a Nijeriya, Ambasada Jesper Kamp.

Fitattun mutanen da suka halarci taron kaddamar da shirin sun hada da gwamnan jihar Abia, Dakta Okezie Ikpeazu da takwaransa na jihar Kebbi Atiku Bagudu da kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni gami da sauran fitattun mutane.

Exit mobile version