Abubakar Abba">

Buhari Ya Kaddamar Da Shirin Daukar Matasa 774,000 A Harkar Noma 

A makon da ya gabata ne, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin noma na matasa a babban birnin tarayyar Abuja, inda Shugaban ya ce, noma ya kasance matsayin tubalin tattalin arzikin Nijeriya, yana mai bayyana shi a matsayin wanda ya fi bayar da gudummawa ga habaka tattalin arzukin kasar.

An kaddamar da shiri ne a karkaahin Hukumar Bunkasa Noma na (NALDA) don sa matasa 1.000 a kowace karamar hukumar yankin 774 a harkar noma.

A wajen taron kaddamarwar wanda ya gudana a Fadar Shugaban Kasa, Buhari ya bukaci hukumomin da ke da ruwa da tsaki a harkar noma da su sake ba da fifiko kan abubuwan da suka sa gaba domin tabbatar da shigar matasa a cikin inganta hanyoyin noma na zamani.

A cewar wata sanarwa daga mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yada labarai Mista Femi Adesina, shugaban ya tabbatar wa dukkan bangarorin da ke da sha’awar shirin cewa za a samar da yanayi mai kyau da ya dace.

Adesina ya ruwaito Buhari yana cewa, “Za mu kara kaimi don fadada zamanantar wa da kuma sauya fasalin noman mu, wanda shi ne mafi mahimmacin ga tattalin arzikin kasar nan, inda ya kara da cewa, na bayar da umarnin a karbo dukkan gonakin Hukumar NALDA da aka kebe don bai wa dubunnan samarinmu maza da mata damar yin noma”.

A cewarsa, “wannan Gwamnatin za ta cimma nasarar samar da aikin gona ne ta wannan hanyar kuma ina da yakinin cewa Nijeriya a karkashin shugabancina, za mu samu wadatar abinci a kasar nan kuma a cikin shekaru masu kyau na girbi muna iya ma fitar da rararmu kuma mu sami kudadwn kasar waje.”

Ya ce, shugaban ya lura cewa sake farfado Hukumar ta NALDA kusan shekaru 20 bayan hakan, za ta ba da tabbacin isasshen abinci yana mai cewa zai kuma zama wani dandamali na samun karin kudaden shiga daga fitar da kayan amfanin gona zuwa kasashen waje a cikin ‘yan shekaru masu zuwa, ya kuma yi alkawarin yin aiki kai tsaye da sanya ido kan hukumar.

Ya kara da cewa, “Saboda tsananin sha’awa da son aikin gona da kuma ni manomi ni kaina, kai tsaye na sa ido a kan Hukumar NALDA a matsayin hukuma a karkashin Fadar Shugaban Kasa, inda ya kara da cewa ina son ma’aikatar noma ta tarayya da gwamnatocin jihohi da su ba Hukumar ta NALDA cikakken goyon baya da hadin kai a kan ayyukanta”.

Ya kara da cewa, nasarar shirin Anchor Borrowers wanda Babban Bankin Nijeriya (CBN) ke jagoranta da kuma sabbin shirye-shirye na farfado da noman Auduga, Kwakwar Manja da kuma koko, nan da ‘yan shekaru masu zuwa za a ga babban bambanci a aikinmu na noma.

A cewar sanarwar, Buhari ya bayar da tabbacin cewa, dukkanin amincewar da NALDA ke bukata don tashi ta yadda ya kamata, wanda ya fara da bangarorin samar da wadataccen filaye don noman amfanin gona da kiwon dabbobi, tuni an ba su.

Ya bukaci Babban Sakatare na Hukumar ta NALDA, Mista Paul Ikonne, da tawagarsa da su ci gaba da rayuwa daidai da tsammanin kuma a lokaci guda su karfafa ayyukansu a cikin al’ummomin yankin, inda ya ci gaba da cewa an sheda min cewa, ya zuwa yanzu, iyalai 4,333 sun ci gajiyar wannan shirin kuma ana sa ran karin mutane da iyalai da dama za su ci gajiyar yayin da aka fara shirin.

Ya ce, yanzu na fidda shirin Matasan Manoma na Kasa wanda ina fata shirin zai dauki matasa ‘yan Nijeriya, da suka kammala karatu kuma ya zama wani bangare na kokarin wannan Gwamnati na rage rashin aikin yi da bada gudummawa wajen farfado da harkar noma da tattalin arzikinmu.

Sanarwar ta kara da cewa, shugaban majalisar dattijan, Ahmad Lawan ya yaba wa shugaban kan jajircewarsa kan sake sanya bangaren noma tun lokacin da ya hau mulki, yana mai cewa kasar ta riga ta ji tasirin manufofin gwamnatin tarayya, inda Lawan ya ba da shawarar bukatar karfafa gwiwar hukumomin aikin gona kamar NALDA don yin aiki tare da cibiyoyin bincike a jami’o’in Nijeriya.

Sanarwar ta kuma ce, iko ne ya gabatar da cewa gano mai a cikin kasar ya dakile ci gaban aikin gona da kuma karuwar talauci a tsakanin al’ummomin karkara.

Amma duk da haka, ya ce Shugaban Kamfanin ya tabbatar wa Buhari cewa kokarinnhada karfi da karfe don farfado da sha’awar noma zai taimaka ta gaske wajen magance talauci da samar da arziki tare da cewa farfado da NALDA zai taimaka wajen rage rashin aikin yi a kasar, musamman a tsakanin matasa.

Ya sanar da cewa, abinda muke mayar da hankali shine mu hada kan manoma 1,000 daga kowace karamar hukumar 774, ta yadda zamu samar da 774,000, kai tsaye a kowani shekara, inda Adesina ya ce, wakiliyar kungiyar Matasan Manoma, Fatima Usman Musa da kuma Jakadiyar Denmark a Nijeriya Jakada Jesper Kamp duo sun jinawa kokarin da gwamnatin take kan yi a fannin na noma.

Sunayen sun hada da gwamnan jihar Abia, Dakta Okezie Ikpeazu, da takwaransa na jihar Kebbi, Mista Atiku Bagudu da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a matsayin wasu fitattun mutane da suka halarci bikin.

Exit mobile version