Buhari Ya Nada Adeyeye A Matsayin Shugabar NAFDAC

Daga Khalid Idris Doya

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya amincewa da nada Farfesa Moji Christiana Adeyeye, a matsayin Darakta Janar na hukumar kula da inganci abinci da kuma kula da magunguna wato (NAFDAC) a Nijeriya.

Bayanin nadin na DG Moji ya fito ne a ranar talata daga wajen mukaddashin Dakaranta Press na ofishin sakataren gwamnatin tarayyar Nijeriya  (SGF) ya ce nadin ya biyu bayan kwarewa da kuma halaye masu kyau da sabowar DG din take da su, a bisa haka ne aka nadata wannan mukamin.

Sanarwar ta ce Farfesa ce a fannin magunguna, kuma kwarrriya ce ta fuskacin ilimin magunguna, masaniya ce akan hada-hadan magunguna, ta kuma halarci manyan jami’o’I ciki kuwa har da na kasar USA inda ya shaida cewar za ta yi kokari wajen tafiyar da ma’aikatar yanda ya kamata.

Ya shaida cewar amincewar da ita da kuma nadin nata ya fara aiki ne a ranar 3,Nuwanba 2017 har zuwa shekaru biyar a matsayin shugaban ma’aikatan NAFDAC.

Exit mobile version