Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Nada Sabon Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya Ta Noma Dake Zuru

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Farfesa Musa Ahmed a matsayin shugaban sabuwar Jami’ar noma ta gwamnatin tarayya dake garin Zuru a Jihar Kebbi.

Nadin na shi yana dauke ne a cikin wata takarda da ministan gona da ci gaban karkara, Alhaji Muhammad Sabo Nanono ya sanyawa hannu.

Kafin ba shi wannan mukamin, Farfesa Ahmed, shi ne Daraktan sashen Kwamfuta da fasahar bayanai (COMSIT) ta Jami’ar Ilorin.

Kuma ya kasance Farfesan a sashen Likitocin Dabbobi, Kwari. Sannan memba ne daga Kwalejin Likitocin Dabbobi ta Nijeriya.

Ita dai sabuwar Jami’ar Noma ta gwamnatin Tarayya dake garin Zuru a jihar Kebbi an tsara za ta fara aiki ne a cikin watan Satumban 2020.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: