Buhari Ya Nemi A Hada Hannu Don Dakile Talauci A Afrika

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci a gaggauta samar da tsari daya domin fuskantar tsananin talauci da rashin aikin yi da kuma samar da karuwar cinikayya tsakanin kasashen Afrika gaba daya.

Mai ba shugaban kasa shawara a bangaren watsa labarai Garba Shehu ne ya bayyana cewar, Shugaba Buhari ya yi wannan tsokacin ne dangane da takardar da shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufu ya gabara a taron shugabannin kasashen Afrika karo na 30 da ya gudana a garin Addissa Ababa ta kasar Ethiopia ranar Litinin da ya gabata.

“Matsayin Nijeriya ne da sauran kasashen Afrika na ganin an tattauna domin samar da tsarin CFTAI, duk da mun kasa cimma wa’adin da kungiyar “African Union” na samar da tsarin a watan Janairu 2012 zuwa shekarar 2017 amma muna da daman kammala tsarin a cikin watan Maris na 2018.

Da ya ke nuna dalilan Nijeriya na amincewa da tsarin CFTA, Shugaba Buhari ya kara bayyana cewa, “A wannan zamani da harkar ci gaban tattalin arzikin duniya ke ci gaba cikin gaggawa samar da tsarin CFTA zai taimaka wa kasashenmu wajen ci gaba da bunkasar tattalin arzikinmu”

Ya ce, tanade-tanaden CFTA na da tsauri amma alfanun ta na da matukar mahimmanci da alfanu daban-daban.

“Samar da hadaddiyar tsarin kasuwanci a Afrika zai tabbatar da samun alfanu a tsakanin kasashen Afrika gaba daya, haddaiyar kasuwa a Afrika zai karfafa kasuwanci tsakanin kasashenmu da kuma fuskantar sauran nahiyoyin duniya a kan harkar kasuwanci” in ji shi

Buhari ya kuma kara da cewa, “In muka kara yawan kasuwancinmu zamu habbaka cikin gaggawa zamu kuma samar da karin aikin yi hakan zai rage talauci a tsakanin mutanemu, abin nufi a nan shi ne tsarin CFTA zai kara dunkule kasashenmu, ya kara hada kanmu da bukasar arzikinmu”

Ya kuma lura da cewa, “Tsarin CFTA zai zo tare da bunkasar masa’anantu da karuwar haraji, hakan zai kuma gaggauta bunkasa tattalin arzikinmu”

Shugaban na Nijeriya ya kuma bukaci takwarorinsa na Afrika da su fadada mahangar su a kan CFTA, “Ba kawai zamu samu bunkasar tattalin arziki kwai ba ne CFTA zai zama wani tsari da zai taimaka wajen dunkuke kasashenmu a matsayin hadaddiya kasar Afrika (African Union)”

Ya kuma kara da cewa, “Samar da CFTA zai zama mataki na farko na cimma burin da aka assasa kungiyar Taraiyar Afirika a kai a ajandan ta na “2063” a taron daya gudana a shekarar 1991 a Abuja.

Shugaba Buhari ya kuma yaba wa Shugaba Issaoufou na jumhoriyar Nijar a kan jajircewarsa na ganin tsarin CFTA ya samu nasarar da ya kamata, ya kuma yaba da kokarin ma’aikatan AU da kungiyar ministocin kasuwanci na Afirika a kan kokarinsu, daga nan ya bukaci daukacin shugabanin kasashen Afrika dasu hada hannu domin ganin tsarin CFTA ya samu amincewar da ya kamata.

 

Exit mobile version