Connect with us

SIYASA

Buhari Ya Nuna Gamsuwa Da Alakar Da Ke Tsakanin Kasar Sin Da Nijeriya

Published

on

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana taron dandalin tattaunawar Sin da Afrika FOCAC, a matsayin kyakkyawar dama ga Nijeriya da dukkanin kasashen Afrika, ta fuskar samun ci gaba da inganta rayuwar jama’arsu.
Cikin sanarwar da mataimakinsa kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ya fitar, shugaba Muhammadu Buhari, ya ce wannan ne karo na biyu da zai halarci taron FOCAC, bayan wanda ya halarta da farko a shekarar 2015 a kasar Afrika ta Kudu, inda ya ce ya tattauna da takwaransa na Sin Di Jinping, game da dangantakar kasashensu, abun da ya kai shi ga ziyartar kasar Sin a watan Mayun shekarar 2016. Ziyarar da ya bayyana a matsayin wadda ta bude kofar samun dimbin damammaki ga kasashen biyu.
Muhammadu Buhari, ya ce yana fatan cimma abubuwan da suka zarta wancan a taron na bana, tare da kara karfafa dangantakar moriyar juna dake tsakanin kasashen 2 da aiwatar da yarjeniyoyin da suka cimma, da kuma rattaba hannu kan wasu sababbi.
Da yake tsokaci game da shawarar shugaba Di Jinping ta gina hanyar kasuwancin siliki ta kan tudu da ta ruwa ta karni na 21, wadda ake kira da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, ya ce kimanin kasashe 90 ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar shiga shawarar da kasar Sin, kuma ita ma Nijeriya ba za a bar ta a baya ba, domin za ta shiga a dama da ita.
Shugaban na Nijeriya ya kuma yabawa ci gaban da kasar Sin ta samu, inda ya ce a bana, kasar Sin ke cika shekaru 40 da aiwatar da manufar bude kofa da gyare-gyare a cikin gida, inda ya ce yunkurin da aka yi a shekarar 1978 ya zama gagarumin aiki a yanzu. Ya ce hangen nesan da ya tabbatar da wannan aiki bayan shekaru 40, ya cancanci yabo, yana mai cewa abu ne dake nuni da cewa, shugabanci na gari da jajircewa, su ne abun da kasa ke bukata idan tana son samun ci gaba, domin kasar Sin ta nunawa duniya yadda ake yi, kuma ya kamata Nijeriya da ma Afrika baki daya su dauki darasi daga gare ta.
Bugu da kari, ya ce kasar Sin ta fitar da mutane masu dimbin yawa daga kangin talauci, kuma ta cimma nasara a fannin fasaha, ta samar da tattalin arziki mai karfi, kana ta sauya zuwa kasar da Sinawa ke alfahari da ita. Ya ce za a iya samun irin wannan a Nijeriya da ma nahiyar Afrika baki daya, domin akwai muhimmin darasin dauka daga manufar kasar Sin ta bude kofa da yin gyare-gyare, kuma za a samu alfanu daga gare ta.
Da ya waiwayi tarihin dangantakar kasashen biyu, ya ce Nijeriya da kasar Sin sun kulla huldar diflomasiyya ne a ranar 10 ga watan Fabrairun 1971. Kuma tun daga wancan lokaci alakar ke kara habaka, inda a yanzu ya kai mataki mai gamsarwa irin na moriyar juna. Ya ce kasashen biyu na mutunta juna, kuma tun daga shekarar 2015 da ya kama aiki, huldarsu ta kara fadada.
Ya ce gwamnatinsa ta kuduri niyyar cika alkawarun da ta dauka lokacin yakin neman zabe, wadanda suka hada da kare kasa da yaki da cin hanci da farfado da tattalin arziki, ta yadda za a samar da aikin yi ga matasa. Ya ce la’akari da matsloli da bukatun jama’a a fannonin ababen more rayuwa, da kuma gano kasar Sin a matsayin wadda ta shiryawa taimakawa ci gaban Nijeriya ne ya sa suka rungumi damarmakin da ta zo da su wajen cike gibin ababen more rayuwa da kasar ke fuskanta.
Ya kara da cewa, ana gudanar da ayyuka da dama a wadancan fannoni, yayin da wasu kuma ake shirin aiwatar da su. Shugaban na Nijeriya ya ce hakika suna godiya sosai ga kasar Sin bisa taimakon da take ba kasar, inda ya ce tana taimakawa da biyan kaso 85 na ayyukan, da kuma bashin da za a dau shekaru 20 ana biya. A cewarsa, babu wata kasa da ta taba yin irin haka.
Ya ce yaki da cin hanci da rashawa na daya daga cikin abubuwan da gwamnatinsa ta sanya gaba, kuma kasar Sin jagora ce a wannan fannin, domin kiyaye doka da oda, muhimmin abu ne a rayuwar Sinawa.
Muhammadu Buhari, ya kuma bayyana cewa, ya gamsu ainun da dangantakar moriyar juna dake tsakanin Nijeriya da Kasar Sin. (Mai Fassarawa: Faeza Mustapha, ma’aikaciyar sashen Hausa na CRI).

Advertisement

labarai