Nasir S Gwangwazo">

Buhari Ya Raba Gardamar Jam’iyyar APC Da Goyon Bayan Giadom

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya fito fili ya raba gardamar da ta barke a cikin jam’iyya mai mulkin kasar, APC, ta hanyar fitowa karara ya bayyana goyon bayansa ga Mukaddashin Sakataren Jam’iyyar na kasa, Mista bictor Giadom.

Bayanin hakan ya fito ne a sanarwar da Mai Magana da Yawun Shugaban kasar, Malam Garba Shehu, ya saki ga manema labarai jiya, ya na mai cewa, Buhari ya dauki wannan matakin ne bayan ya nemi shawarar masana shari’a.

“Shugaban kasa ya amshi gansasshiyar shawarar kwararru ta fuskar shari’a, wanda ya nuna cewa, doka ta na bayan bictor Giadom a matsayin Shugaban Riko na kasa,” in ji shi.

Advertisements

Sanarwar ta kara da cewa, “don haka, kasancewar a kowane lokaci ya na daukar matakansa ne daidai da shari’a, Shugaban kasar zai halarci taron da Giadom ya kira a gobe (yau Alhamis) ta hanyar bidiyo.”

Ya kuma ce, shugaban ya na sa ran gwamnoni jam’iyyar da jagororinta na Majalisar Dokoki ta kasa za su halarci za su samu halartar ganawar. Daga nan sai ya yi kira ga kafafen yada labarai da su daina kirikrar karairayi kan batun ta hanyar bayar da fassarori marasa kan gado.

Idan dai za a iya tunawa, APC ta fada rikicin shugabanci ne tun bayan da wata Babbar Kotu a Abuja ta tabbatar da dakatar da Shugaban Jam’iyyar na kasa, Mista Adams Oshiohmole, kwanakin baya, inda rikicin wanda zai maye gurbinsa balle tsakanin wasu bangarori.

Exit mobile version