Buhari Ya Soke Ganawarsa Da Ministoci Yau

A yau Laraba shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya soke ganawarsa da ake sa rai zai yi da ministoci, mai magana da yawon shugaban kasa Femi Adesina ne ya sanar da hakan a safiyar yau, ganawar wacce ake yinta duk ranar Laraba.

Ganawar  ita ce ta farko tun dawowar shugaban daga jinya a birnin Landan, a lokacin da shugaban kasar baya kasar, mukaddashin shugaban kasa Yemi osinbajo ne ke jagorantar ganawar fiye da watanni uku.

Shugaba Buharin ya dawo aiki ne ranar litinin.

Exit mobile version