Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Soke Kwangilar Dala Milyan 195 Da Ameachi Ya Ba Kasar Isra’ila

Published

on

A farkon wannan makon ne, Shugaba Buhari ya soke sabuwar kwangilar samar da tsaro wacce manyan jami’an gwamnatinsa suka bayar a bisa dalilin tafka mummunan magudi a cikinta.

Kwangilar, wacce Jami’an gwamnatin na shi suka sanya wa hannu a watan Disamba 2017, ta baiwa dan kwangilar na kasar Isra’ila, HSLi, damar kwasan tsabar dala milyan 195, bisa sharadin zai kawo wani adadi da ba a tantance ba na Jiragen sama, Jiragen Helikwafta da Jiragen ruwa 12 ga rundunar tsaro ta ruwa, da za su gudanar da wani aiki na musamman.

Akwai Son Rai A Cikin Kwangilar?

Ministan Zirga-Zirga, Rotimi Amaechi ne ya daddale kwangilar, amma sai Majalisar Wakilai ta tarayya ta saka ayar tambaya kan yadda aka bayar da kwangilar, da ma ainihin sanin wanda aka baiwa kwangilar.

Cikin sakon da shugaban ma’aikata na fadar ta shugaban kasa, Abba Kyari, ya aike, ya umurci babban mai shari’a na kasa, Abubakar Malami, da ya dakatar da kwangilar, hakanan shugaban kasan ya umurci mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, da hukumar binciken sirri ta kasa da su binciki yadda aka yi har dan kwangilar ya sami kwangilar ba tare da yana da cikakkun takardu ba.

Shugaban kasan ya umurci dan kwangilar da ya tabbatar da ya kawo kayan dala milyan 50 na somin tabi da ya fara lasawa kwanan nan.

Dan kwangilar, HSLi, ya shigo ne a matsayin shi wani kamfani ne na kasar Isra’ila, wanda Ministan na Zirga-Zirga ya kawo shi, wanda kuma ba shi da rajistan irin wannan aikin a kasar ta Isra’ila, sai dai su na da kusanci sosai da wani kamfanin na kasar ta Isra’ila mai suna, Mitrelli, kamfanin da ke da alaka ta kud-da-kud da Ministan na Zirga-Zirga.

A shekarar 2012, lokacin da Amaechi ke gwamnan Jiha Mai arzikin Man Fetur ta Ribas, ya baiwa wannan kamfanin na Mitrelli (Wanda ake wa lakabi da LR Group) kwangilar dala milyan 140 domin habaka wata gona a Etche, wacce ke bayan garin na Fatakwal.

Abin da ya kawo zargin

Jim kadan da bayar da kwangilar ne masu suka su ka fara zargin gwamnati da cewa, yin hayar wani kamfanin waje domin ya samar da tsaro a tekun Nijeriya, hakan zai iya sance ikon da tsaron da Nijeriya ke da shi a kan ruwayen na ta.

Majalisar Wakilai kuma ta kaddamar da bincike kan aikin kwangilar sabili da koken da wasu kungiyoyi suka kai mata na cewa akwai rufa-rufa a cikin kwangilar.

Majalisar Wakilai

A watan Maris  ne kwamitin sauraron koke-koke na Majalisar ta Wakilai, wanda ya binciki kwangilar ya shaidawa Majalisar cewa, tabbas akwai harkalla a cikin kwangilar, kuma kwamitin ya nemi Majalisar da ta hanzarta dakatar da kwangilar.

‘Yan Majalisar suka ce, HSLi, ba shi da rajistan aikin samar da tsaro a kasar ta Isra’ila, sannan kumaAmeachi, ya kasa kawo takardun kwangilar duk da damar sauraron sa kan hakan sau takwas da Majalisar ta ba shi.

A lokacin da binciken kwamitin ke ci gaba da gudana, Ameachi ya ce wai wasu lalatattun mutane su na ta yunkurin ganin sun dakatar da aikin kwangilar saboda su na cin gajiyar halin rashin tsaron da ke gudana a halin yanzun.

“Ba zan fadi ko su wane ne ba, har sai abin ya kai makura,” in ji Ameachin a wani taro da aka yi a Warri cikin watan Fabrairu. “Har yanzun muna fafutukar ganin an fara aikin kwangilar ne, amma idan har sun dage, za mu shaidawa duniya ko su wane ne, har ma da Jami’an tsaron cikin su.

“Mutane ne da suke samun bilyoyin daloli na haram a tafkunan namu, don haka ne ba sa son aikin kwangilar samar da tsaron a tafkunan namu ya samu, duk za mu yi maganin su. In ji Ameachi.

Sai ya kirayi masu mallakan Jiragen ruwa da kuma sauran masu aiki a tashoshin Jiragen ruwan namu da su kai koke wajen Shugaban kasa, domin aikin kwangilar da ya sanya wa hannu ya tabbata.

Babu tabbacin ko da ‘yan Majalisun ne Ameachi ke wannan shaguben a wancan lokacin.

Binciken da fadar Shugaban kasa ta kafa

Dakatar da aikin kwangilar da gwamnati ta yi kwanan nan, ya baiwa ‘yan Majalisar bugun kirji da nu na kansu, a matsayin masu gaskiya.

A daidai lokacin da gwamnati ke gudanar da binciken, sai hukumar NIMASA ta bukaci da rundunar Sojin ta ruwa da ta gabatar da bukatun ta na kayan tsaro.

Kasantuwar irin dogon burin da Amaechi ya sanya kan wannan aikin kwangilar, dakatar da kwangilar wani babban hari ne a gare shi, in ji wata majiya ta Soji.

“Ministan ya sanya mu a cikin aikin kwangilar,” in ji wani babban jami’in rundunar Sojin ruwan da ba ya son a ambaci sunan sa, kamar yadda ya shaida wa kafar yada labarai ta, ‘PREMIUM TIMES,’ a ranar Juma’a da dare. “Ya yi duk abin da zai iya yi sai da ya tabbatar da Shugaban kasa ya sanya hannu a kan kwangilar, amma ga alama daga baya Shugaban kasan ya gano cewan an yaudare shi ne, da ya fahimci akwai alamun rufa-rufa kan abubuwa ma su yawa a cikin kwangilar.”

Masu magana da yawun Shugaban kasan, Femi Adesina da Garba Shehu, duk sun ki amsa sakonnin da muka yi masu sun kuma ki amsa waya, domin neman karin bayanin ko Shugaban kasan ya sanar da Ameachi kafin ya soke kwangilar.

Wani mai magana da yawun Ma’aikatar ta Zirga-Zirga, Yewande Shonaike, shi ma ya ki ya ce uffan kan yadda Ma’aikatan na su ta ji da soke wannan kwangilar. Da jimawa dai ana ganin Ameachi a matsayin na hannun daman Shugaba Buhari ne a gwamnatin na shi, ana kuma daukan shi a matsayin wani babban jigo na kokarin sake zaben Buharin.

A shekarar da ta gabata ne, Buhari ya sake jaddada cewa, Ameachi ne sarkin yakin neman zaben na shi a 2019.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: