Umar A Hunkuyi" />

Buhari Ya Taya Nasir el-Rufa’i Murnar Cika Shekara 60 A Duniya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bi sahun al’ummar Jihar Kaduna wajen taya Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, murna cika shekaru 60 da haihuwa a ranar Lahadi mai zuwa.

Cikin sakon taya murnar da shugaban kasan ya aike wa gwamnan na Jihar Kaduna, ta hannun mai ba shi shawara ta musamman a kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina, a Abuja ranar Asabar, yana taya gwamnan murna ne a bisa hidimar da yake yi wa kasa.

Buhari ya taya iyalan gwamnan da abokanan sa murna, ya kuma nanata aniyar sa ta samar da canji da kuma shugabanci nagari wanda hakan yake karfafan matasa da shi. A cewar Shugaban kasan, hangen nesa irin na Nasir el-Rufai, da kuma hikima abu ne wanda yake ci gaba da karfafan al’umma wajen tabbatar da fatan sa, wanda kuma hakan ne ya bambanta shi da sauran shugabanni.

Ya kuma yi nuni da cewa, shigan Nasir el-Rufai, cikin harkokin siyasa ya zo ne a bisa hadari, “Amma dai gudummawar da ya bayar a tsarin sun tabbata har ya zuwa tsawon zamani. A cewar shugaban kasan, gudummawar na shi sun kuma taimaka matuka wajen samun nasarar zaben shekarar 2015, wanda hakan ya kai ga samun nasarar Jam’iyyar APC.”

Shugaban kasan ya yi addu’an Allah Ya ci gaba da albarkatan gwamnan da iyalansa, ya kuma kare shi da lafiyar da zai ci gaba da ayyukan alheran da ya faro.

Exit mobile version