- Karancin Kudin Shiga Ya Tilasta Mu Cin Bashi, In Ji Shi
Daga Khalid Idris Doya,
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya shaida cewar gwamnatinsa na ciwo bashi ne domin tallafa wa karfafa tattalin arziki gami da cigaba a sakamakon raguwar samun kudaden shiga.
Da ya ke jawabi a jiya Alhamis yayin tattaunawa ta farko kan haraji na kasa wanda ya gudana a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja, Shugaba Buhari, ya kuma bukaci hukumar tara kudaden haraji ta kasa (FIRS) da sauran hukumomin gwamnati da su tashi tsaye kana su fito da tsare-tsare da shirye-shiryen da suka dace domin bunkasa sashin kudaden shiga wa kasa.
A cewarsa, FIRS dole ta tabbatar da toshe dukkanin gibin da ke akwai a sashin haraji tare da tabbatar da masu biyan haraji suna biya yadda ya kamata gami kuma da tabbatar da kamfanonin kasashen waje da suke cin moriyar Nijeriya su ma kansu suna biyan haraji yadda aka tsara, ya kuma nemi a kara samar da hanyoyin zamani da hadin kai domin kyautata sashin tara kudaden haraji.
Shugaban, ya nemi ‘yan Nijeriya da su rungumi dabi’ar biyan haraji yadda ya dace domin a cewarsa biyan haraji sadaukarwa ne da ‘yan kasa na hakika ke yi domin cigaba da samar da ayyukan raya kasa.
Buharin ya ce, gwamnatinsa babu makawa ta amshi bashin ne domin cike gibin kasafin sakamakon karancin kudin shiga a wasu shekaru wanda hakan ya kara yawan kudaden bashi da ke kan Nijeriya.
“Wannan shi ne ya janyo aka samu karin kudin da ake bin Nijeriya bashi wanda ya haura tiriliyan N32tr a Satumban 2020. Wannan gibin kudin da aka samu ya faru ne sakamakon karancin kudaden shiga na haraji, don haka, muka ga dacewar mu shirya taron tattaunawa kan haraji wanda muka yi a yau.
“Babu wata kasa da ta samu cigaba ba tare da biyan kudin haraji ko yin sadaukarwar da ya dace ba. Don haka, ina kira ga ‘yan Nijeriya da suke raye da su rika biyan haraji. Wannan gwamnatin za ta fito da tsare-tsaren kyautata hanyoyin tara kudaden haraji daidai da tsarinmu na haraji.
“Kan wannan, FIRS da ta tashi tsaye wajen yin duk mai yiyuwa domin taskace hanyoyin amsar kudaden haraji daga wajen masu biya na ciki da na waje ta hanyar yanar gizo. Gwamnatinmu ta yi kwaskwarima wa dokokin kudi na 2020 wato Finance Act 2020,” a cewar Buhari.
Shugaban ya umarci dukkanin hukumomi da ma’aikatun gwamnati da su samar da hanyoyin gudanar da ayyukan kai tsaye domin tabbatar da taimakawa sashin haraji na kasa.
“Bai wadatar ba a ce ‘yan kasarmu da ‘yan kasuwanmu su biya kasonsu na haraji. Amma a samu tangarda daga kamfanonin kasashen waje. Don haka kamar na cikin gida, su ma masu kasuwanci ‘yan kasashen waje ba za mu basu damar cigaba da kwasar garabasa a kasuwanninmu da tattalin arzikinmu ba tare da biyan haraji yadda ya dace ba.
Buhari ya kuma nemi hukumomi da su yi amfani da sabbin fasahohi wajen tattawa da kuma biyan kudin haraji yadda ya dace, sai ya nemi hukumar tara kudin haraji na kasa da su nazarci nagartattun hanyoyin da suka dace wajen ganin an kyautata sashin biyan kudin haraji.
Shugaban ya kuma ce, Nijeriya za ta ci gaba da aiki wajen samar da tsare-tsaren da suka dace tare da tabbatar da samar da tsare-tsaren da za su yi daidai da matakin kasa da kasa gami kuma da zamanantar da sashin tara kudin haraji, ya nuna fatansa na cewa a shekarar 2021 za a samu kyautata sashin kudin haraji yadda ya dace.
Shugaba Buhari, ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta cigaba da kokarin tabbatar da kyautata rayuwar jama’a ta hanyar samar da tsare-tsaren aiwatar da ayyuka da suka hada da na layin doguwa, gina hanyoyi da kwaskwarima ma wasu, samar da wutar lantarki, kiwon lafiya da na ilimi, duk kuwa da kalubalen kudin haraji da na annobar da Korona ta haifar.
“Gwamnatinmu za ta ci gaba da tabbatar da ayyukan da ake yi sun samu nasarar kammaluwa gami da samar da wasu ma duk da annobar Korona.
“Annobar Korona ya tagayyara sashin lafiya da tattarzikin duniya. Kamar kowace kasa, muma tattalin arzikinmu bai tsarkaku daga fadawa wannan karayar da annobar ta jawo ba.
“Kan hakan, dole mu fuskanci hanyoyin da za mu samu fita daga tagayyarar tattalin arziki a gefe guda kuma dole mu fadada hanyoyin kudin shiga domin cimma tsarin da aka samar a kasafin kudi. A cikin wannan yanayin ne gwamnati ta samar da ayyukan da suke cikin kasafin kudi na sama da tiriniyan 13 a kasafin 2021,” a cewarsa.
Ya nemi ‘yan Nijeriya da su maida hankalinsu wajen biyan kudaden haraji gami da cewa hakan shine zai bada damar gwamnati ta samu damar gudanar da dukkanin ayyukan raya kasa da al’ummarta.
Ya kuma yi batun cewa dokar da aka sanya wa hannu na kudi ta 2020 zai taimaka sosai wajen kyautata sashin kudaden shiga da kuma saukaka wa masu biyan haraji bi din cikin sauki.
A jawabinsa da ya gabatar, shugaban Banki raya shiyyar Afrika (AfDB), Dakta Akinwunmi Adesina, ya yi hasashen tattalin arzikin Nijeriya zai fita daga matsatsin tattalin arziki, tare da karuwar kashi 1.5 a 2021, da kuma kashi 2 a 2022.
Dakta Adesina, ya shaida cewar ya kamata a yi amfani da haraji wajen gudanar da ayyuka tare da karfafan kamfanoni masu zaman kansu da suke maida hankali wajen biyan kudin haraji a kai a kai.
Ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, ta shaida cewar gwamnati za ta inganta hanyoyin amsar kudaden haraji, musamman ma lura da karancin samun kudin shiga duk kuwa ta barnar da annobar Korona ta jawo wa tattalin arziki, ta nuna cewa shekarar 2021 za ta kasance shekarar farfadowa daga sumar da aka fada kan tattalin arziki.