Shugaban Nijeriya, Alhaji Muhammadu Buhari, ya yi ta’aziyyar rasuwar gwamna na farko a zamanin mulkin soji daga shiyyar Arewa Maso Yamma, Alhaji Usman Faruk.
Wakilinmu ya nakalto cewa, marigayi Usman Faruk dai tsohon kwamishinan ‘yan sanda ne, ya rasu ne a shekaran jiya 18 ga watan Disamba. An haifesa ne a shekarar 1935 a garin Gombe, ya zama gwamnan mulkin soja ne a yayin mulkin shugaban kasa a zamanin soja Yakubu Gowon.
A sanarwar da shugaban ya fitar ta hannun hadiminsa, Mallam Garba Shehu, Buhari ya shaida cewar tsohon kwamishinan ‘yan sandan ya himmatu wajen hada kan kasa da ‘yan kasa a lokacin da yake raye.
“Shugaba Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai, ‘yan uwa da abokan marigayi gwamnan farko a zamanin mulkin soji na shiyyar arewa maso yamma, Alhaji Usman Faruk, bisa rasuwa da Allah ya masa.
“Sannan, Shugaba Buhari ya kuma lura da irin kwazon marigayi Alhaji Usman Faruk ta fuskacin bunkasa al’ummarsa har zuwa bayan lokacin da ya yi ritaya, ya nanata cewa marigayin ya kasance mai kwatanci da kyawawan ayyuka gami da hidintuwa wa al’umma.
“Buhari yana masa addu’ar Allah ya jikansa ya sanya aljannace makomarsa, sannan yana addu’ar Allah albarci iyalan da ya bari,” inji sanarwar.
Tun bayan rasuwarsa ne dai wakilinmu ya shaida mana cewar al’umma ke ta cinciridun mika ta’ziyyar rashinsa a jihar gwamna, inda fitattun mutane da dama suka yi ta nuna alheninsu da wannan babban rashin.