Buhari Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Mai Tsaron Ragar Super Eagles

Tsaron Raga

Shugaban kasa Mohammadu Buhari ya aike da sakon ta’ziyarsa dangane da mutuwar tsohon mai tsaron ragar Super Eagles, Joe Erico, wanda ya mutu a gidansa a satin da ya gabata yana da shekaru 71 a duniya bayan gajeriyar rashin lafiya.

A cikin wata sanarwa da mai taimakawa shugaba Buhari kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya fitar mai taken “Joe Erico” Shugaba Buhari ya jajantawa danginsa da hukumar NFF kan mutuwar Joe Erico,” Shugaban ya ce ya yi bakin cikin samun labarin.

Erico na daga cikin masu horar da babbar tawagar ‘yan wasan Najeriya ta Super Eagles a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta shekarar 2000 da aka yi a Lagos, kuma ya taimaka wa Najeriya ta samu tikitin shiga gasar Afcon da kofin duniya a shekarar 2002.

Tsohon kocin wanda masoyansa ke wa lakabi da ‘Jogo Bonito’ wato wani salon wasa da aka san Brazil da shi na tattaba kwallo, ya rasu ne a jihar Lagos bayan gajeriyar rashin lafiya kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

A safiyar Alhamis din nan ne jami’in yada labaran tawagar Super Eagles, Babafemi Raji ya tabbatar da rasuwar tsohon mai tsaron ragar inda kuma tuni hukumar ta NFF ta aiki da sakon ta’aziyyar mamacin ga iyalansa.

Erico ya fara sana’arsa ta kwallon kafa ne da kungiyar kwallon kafa ta ‘yan sanda, wato Nigerian Police Force, sannan ya buga wasa a kungiyoyin Nepa da Railways Electricity Connectors da kuma kungiyar Julius Berger.

Sannan Joe Erico ya horar da kungiyar kwallon kafa ta Julius Berger da kungiyar Stationery stores duk a jihar Lagos, sai Mighty Jet ta garin Jos da sauran su duka a lokacin da yake harkar wasanni a Nigeria.

Exit mobile version