Buhari Ya Yi Wa Manyan Jami’an Soja Biyu Karin Girma

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa wasu manyan jami’an Soja karin girma na musamman saboda gagarumar rawar da suka taka wajen aikin samar da tsaro. Sanarwar da Kakakin rundunar Soja ya fitar, Kanar Sagir Musa ya ce an karawa Manjo Janar Lamidi Adeosun girma daga mukaminsa na yanzu zuwa Laftanar Janar, yayin da aka karawa Kwamandan runduna ta 7 Birgediya Janar Abdulmalik Bulama Biu girma zuwa Manjo Janar.

Sanarwar ta kuma ce an karawa Laftanar AJ Danjibrin girma zuwa Kaftin.

Sanarwar ta kuma ruwaito babban hafson sojin Nijeriyar Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai na ta ya murna ga hafsohin dangane da karin karin girmar.

Exit mobile version