Bello Hamza" />

Buhari Ya Yi Wa Sultan Ta’aziyyyar Rasuwar Dan Uwansa

Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyar rasuwar Alhaji Abdulkadir Jeli Abubakar, Dikkon Sakwatto kuma kwamishinan cikin gida na jihar Sakkwato.

Marigayin kuma dan uwa ne ga Sultan na Sakkwatto, Alhaji Sa’ad Abubakar III.

Malam Garba Shehu, jami’n watsa labarai ga shugaban kasa ne ya bayar da sanarwa ta’aziyyar a takardar sanarwar da ya raba wa manema labarai a garin Abuja ranar Juma’a.

Shugaban kasar ya ce, ’Na samu labarin rasuwar cikin jimami da kaduwa, na marigayi Alhaji Jeli Abubakar.

”Muna addu’ar Allah ya gafarta masa ya kuma sanya shi a gidan al’janna, ya kuma baku hakurin jure wannan rashi na dan uwan na ka.”

Shugaba Buhari ya kuma mika ta’aziyya ga gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal da al’ummar jihar gaba daya.

Exit mobile version