Ministan Zirga-zirga, Rotimi Amarchi, ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya tana nazarin kara ciwo sabon bashi domin ta gudanar da wasu ayyukan gina hanyoyin Jiragen kasa.
A ranar Talata ne Ministan ya fadi hakan, jim kadan bayan ganawar da ya yi da Shugaban kasa a fadar gwamnati ta Aso Billa, Abuja.
Mista Amaechi, ya ce, Shugaban kasan, ya bayar da izinin a tattauna kan ciwo bashin dala bilyan 15 domin gina hanyar Jirgin kasan da ta tashi daga Fatakwal zuwa Maiduguri da ta Legas zuwa Kalaba.
“Hanyar Jirgin ta Legas zuwa Kalaba, ko fara ta ba a yi ba, saboda ba kudi, ita ma ta Fatakwal zuwa Maiduguri ba a fara ba, saboda matsalar kudin, amma Shugaban kasa ya yarda da mu tattauna kan ranto kudaden.
“Mun kusa ma kammala tattaunawa kan ta Fatakwal zuwa Maiduguri. Muna neman kudi ne da suka kusanci dala bilyan 14 zuwa 15,” in ji Ministan.
Amaechin kuma ya ce, za a fara shimfida titin Jirgin na tsakanin Legas zuwa Ibadan a watan Afrilu.
Ya nu na sa ran da yake na kammala aikin a karshen watan Janairu na shekarar 2019.
Ya ce, hakan zai samarwa ‘yan Nijeriya da ayyukan yi.
“Muna sa ran kimanin Tan 6,000,000 na kaya daga cikin tan 30,000,000 na kayan da muke da su a tsakanin Legas da Kano.
“Aikin kuma zai samar da dubannan ayyukan yi.