An bayayyana cewa, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari zai rattaba hannu a kasafin kudin shekarar 2021 a yau Alhamis.
A ranar Litinin da ta gabata ne majalisar kasa ta amince da kasafin kudin shekarar 2021 na Naira tiriliyan 13.58. Shi dai kasafin kudi abin da gwamnati ne za ta kashe tun daga watan Junairu har zuwa watan Disamba wajen gudanar da ayyukan ci gaban kasa. A ranar 17 ga watan Disambar shekarar 2019, shugaban kasa Buhari ya rattaba hannu a kasafin kudin shekarar 2020, wanda ya zama doka. Ana saran wannan kasafin kudin zai amfani ‘yan Nijeriya wajen magance musu matsalolin da ke addabar su a cikin kasar nan. Ana fatan a ranar Alhamis kasafin kudin shekarar 2021 ya zama doka idan aka rattaba hannu kuma ya kasance rana ta karshe ga kasafin kudin shekarar 2020.
Mashawarcin shugaban kasa ta fannin yada labarai, Garba Shehu shi ya tabbatar wa manema labarai hakan a ranar Talata da yamma.
“Komi zai dai-daito, domin shugaban kasa zai rattaba hannu a kasafin kudin shekarar 2021 a ranar Alhamis.
Mafi yawancin ana shirya kasafin kudi ne ta hanyar gabatar da daftari a gaban majalisar kasa wanda shugaban kasa yake kaiwa, ana samun daftarin ne ga kudaden da ma’aikatu da rassa da hukumomin gwamnati za su kashe a shekara.
Wata majiya daga fadar gwamnati wadda ta bukaci a sakaye sunanta saboda ba a hukumance lamarin yake ba, ta bayyana wa manema labarai cewa, an kammala duk wani shirye-shirye na kasafin kudin shekarar 2021. Majiyar ta bayyana cewa, a ranar Alhamis shugaban kasa zai rattaba hannu a kasafin kudin wanda zai aika wa majalisa kofin kundin idan ya rattaba hannu a cikinsa.
A ranar Litinin ce, majalisar kasa ta amince da kasafin kudin shekarar 2021 na naira tiriliyan 13.08 wanda ta kara sama da biliyan 500, inda ya koma naira tiriliyan 13.59.
A ranar 8 ga watan Oktobar shekarar 2020, shugaban kasa ya gabatar da kasafin kudin a gaban majalisun kasa guda biyu. Dukkan majalisun kasa wadanda suka hada da majalisar dattijai da majalisar wakilai sun gudanar da bincike a kan kasafin kudin kamar yadda doka ta tanada kafin a tafi hutun kirsimeti da sabon shekaran da za a shiga. A cikin kasafin kudin shekarar 2021 na tiriliyan 13.59, za a biya bashi da naira tiriliyan 3.32, za a kashe naira tiriliyan 5.64 wajen biyan albashi, yayin da za a kashe naira tiriliyan 4.13 wajen manyan ayyuka.