Buhari Zai Sake Ciyo Bashin N11trn Don Cike Gibin Kasafin Kudin 2023
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Buhari Zai Sake Ciyo Bashin N11trn Don Cike Gibin Kasafin Kudin 2023

byMuhammad
3 years ago
Buhari

Gwamnatin Tarayya ta ce da yiwuwar zata sake ciyo wani bashin na Naira tiriliyan 11.3 don cike gibin kudaden shigar da za ta samu a kasafin kudin 2023.

Aminiya ta rawaito cewa, ciyo bashin na nufin gibin ya zarce na kasafin 2022 na Naira tiriliyan 7.35 da fiye da kaso 100.

  • “Ba Zan Mara Wa Atiku Ko Wani Dan Takara Na Kyale Tinubu Ba” —Buhari
  • ‘Yan Ta’adda Ba Rauhanai Ba Ne, Dole Sojoji Su Yi Maganinsu – Buhari

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ce ta sanar da haka, lokacin da take gabatar da daftarin matsakaicin tsarin kashe kudade (MTEF&FSP) na shekarun 2023 zuwa 2025, a gaban Kwamitin Kudi na Majalisar Wakilai ranar Litinin.

Zainab ta kuma ce la’akari da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, ana hasashen cewa gibin kasafin zai kai kusan Naira tiriliyan 12.41, a maimakon tiriliyan 7.35 na kasafin 2022.

Ta kara da cewa, “Jimillar kudaden da ake sa rai Gwamnatin Tarayya za ta kashe a 2023 su ne tiriliyan 19.76.

“A cikin haka kuma, ana hasashen gibin kasafin ya kai tiriliyan 11.30 a 2023, kari a kan tiriliyan 7.35 na kasafin 2022.

“Hakan na nufin kaso 5.01 na ma’aunin tattalin arziki na GDP, wanda kuma ya haura kaso uku cikin 100 da aka tanada a Dokar Kashe Kudade (FRA), ta 2007,” inji Zainab.

Dangane da batun tallafin mai kuwa, Ministar ta ce akwai yiwuwar gwamnatin ta kashe Naira tiriliyan 3.36 ko kuma tiriliyan 6.7 a 2023.

Sai dai ta koka cewa kudaden da Najeriya ke samu daga cinikin danyen mai na raguwa duk kuwa da farashinsa na karuwa a kasuwar duniya.

Ta alakanta hakan da kalubalen da ake fuskanta wajen hako man da kuma yawan kudaden da NNPC ke kashewa wajen biyan tallafi.

Kazalika, Ministar Kudin ta koka cewa duk da Nijeriya na kashe Naira biliyan 3.2 wajen gadin bututan mai, kwalliya ba ta biyan kudin sabulu.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar, James Abiodun Faleke, ya ce la’akari da halin da Nijeriya ke ciki, ya zama wajibi ta lalubo dukkan hanyoyin fadada kudaden shigar ta.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
Ra’ayoyinku A Kan Ruwan Sama Marka-marka Da Ake Yi A Sassan Nijeriya

Za A Sake Jera Kwana Hudu Ana Zabga Ruwan Sama A Jihohin Arewa Biyar - NiMet

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version