Connect with us

TATTAUNAWA

Buharin Ya Yi Kokari A Harkar Tsaro, Amma –Husaini Gambo

Published

on

Wannan wata tattaunawa ce da wakilinmu a Yola ya yi da Shugaban kungiyar Adamawa ‘Consent Citizen Foundation,’ kuma dan ga-ni kashenin Shugaba Buhari a zaben 2015, Hussaini Gambo Nakura. A cikin tattaunawar ya nuna bada kai bori ya hau da Shugaba Buhari ya yi game da rikita-rikitar jam’iyyar APC da cewa abin kunya ne. Mun kuma tabo batun almundahana da rahoton kwamitin Justis Bobbo Umar ya bankado kan tsohowar gwamnatin Murtala Nyako.

Ga dai cikakkiyar tattaunawar. A Sha karatu lafiya. Ga dukkan alamu Shugaba Muhammadu Buhari ya bada kai bori ya hau. Me kake ganin zai faru?

Eh toh. Na farko dai zan yi addu’a Ubangiji Allah ya kawo mana zaman lafiya, da irin halin da kasar nan take ciki, na abubuwan da ke faruwa a Zamfara da kashe-kashen ‘yan Adam da ake yi, kusan Alhamdu lillah Allah ya kawo mana sauki a maganar Boko Haram. Allah ya kawo sauki akan Iyamurai masu son su raba Nijeriya su dauki bangarensu, sun ga abin ba zai yiwu ba. Sannan kuma Allah ya kawo sauki a wasu fitinu da ake yi kamar na Fulani makiyaya da manoma.

Abin da zan yi magana a nan, mu dai mu muka zabi Buhari, da kori’unmu, amma mu Buharin da muka zaba yanzu ba shi ne yake kan kujera ba. Wato mun ga Buharin da muka sanshi a da, mai magana guda daya mai ra’ayi daya. Don haka talakawan Nijeriya suka rinka saka masa kudadensu suka rinka bada karfinsu domin su zabeshi, sun zabeshi ya zama shugaba, amma Buhari ya karkace ya zama Bayarbe.

 

Ta yaya?

Ehmana! Abin da na gani, Buhari yana zaune a inda aka yanke hukuncin na jam’iyyar APC, bayana da yana zaune aka yanke hukuncin zai zama abin mamaki ga dukkan wani dan Nijeriya a wayi gari a ce wannan Buharin ne kuma shi zai fita ya ce abin da aka yi ba a yi daidai ba, a yi gyara saboda ra’ayin mutum daya tak, shi ne Bola Ahmad Tinibu, ra’ayin Tinibu ne  Buhari yake bi, ba ra’ayin ‘yan Nijeriya ba, don jam’iyya tana da tsarinta wadanda aka tara a jam’iyyar gaba daya a hada su don son zuciya su ce sun kara wa Shugabanni wani lokaci, a wayi gari don mutum daya ya ce bai yarda ba a dawo kan abin da ya fada? Wannan ya nuna mun gane Tinibu ne yake mulkin Nijeriya.

Ke nan kun cire fata daga shugabancin Shugaba Buhari?

Wato idan ana maganar gaskiya, ya kamata Buhari ya dawo ya yi tunani, Tinibu ba ya bada mulki, Allah ne ke bada mulki. Buhari ya tsaya sau hudu, kuma a addini ma Annabi (S) ya ce ‘Maciji ba ya cizon mumini sau biyu a rami guda.’ Amma Buhari ya kai hannunshi har sau uku ana saranshi yana maidawa har ya samu ya kamo. To idan ka duba, Allah kadai ya fi sanin dalilin da ya sa ya baiwa Buhari mulkin Nijeriya, ko ya gyara ko ya bata. Idan ya yi gyara, ya tsira da mutuncinsa daga duniya har lahira, idan ya bata, ya bata daga duniya har lahira. Domin yanzu haka a Arewa jihohi da yawa wadanda ba sa samun wuta, amma Kudu suna samun wutar lantarki.

 

Na san kai na gaban goshin Buhari ne da kuka jajirce domin ya samu nasara a zaben 2015, sai ga shi ka fito kana irin wadannan kalaman?

Eh, wato abin da ya sa zai yi irin wadanan kalaman, na yi kalaman ne saboda Buhari yana son ya cucemu mu ‘yan Arewa. Ai Tinibu ya fita ya ce ba su yi haka da Buhari akan matsayin zabe na biyu ba, baya goyon bayansa, Gwamnoni kuma sun ga kuran da Buhari ya daure, idan ba shi, ba babu mai kwancewa. Yarabawa da bakinsu suka sa man fetur ya koma Naira 145, su suka sa aka cire tallafin Taki, aka cire tallafin mai, suka sa Buhari ya cire duk wani tallafin da talaka zai ji dadi.

Talaka sun ki su yi wa Buhari zanga-zanga ne saboda suna sonshi, lokacin har Labor suna son su yi masa zanga-zanga, talaka sun ki su baiwa Labor goyon baya. Da bakin Buhari ya ce idan talaka ya sayi man fetur Naira 50 a lokacin Goodluck talakan Nijeriya ba a kyauta masa ba, sai ga shi Allah ya baiwa Buhari mulkii, sannan ana bukatar wadannan da suke kan kujerar nan dole za su iya maida Buhari don jam’iyya ta bar hannun su Tinibu. Amma idan aka ce an kawo rudani a cikin jama’iyya, su burinsu ya biya sun yi amfani da Buhari ya cutar da Arewa. Saboda haka kuma za su karbi mulki in sun karba a hannunsa me dan Arewa ya isa ya fada? Ba abin da dan Arewa ya isa ya fada!

 

Yaya kake jin makomar APC zai kasance?

Ai shi ne nake gaya wa Buhari, ina gaya wa Buhari ne ya sani duk abin da ya tallafa na tallafin da zai taimaki talakawa fa, dayake cewa talakawa masoyansa ne, kada ya yarda ya tsaya da su a gaban Ubangiji, don in ya tsaya da su a gaban Ubangiji ba zai ji dadi ba, don talakan Nijeriya sun so shi sun yarda da shi, kuma sun yi Imani akan cewa zai kawo musu canji. A lokacin Goodluck ana tafiya Hajji da tsada, Naira Dubu Dari Bakwai, amma yau Buhari yana kan mulki yana gani sai ka biya Naira Miliyan da da Dubu Dari biyar ko Dari shida.

Yana kallo ana cewa tattalin arzikin kasa ne ya karye, wadannan duk su suke bukata sun yarda akan cewa lallai Buhari ya yi musu abin da suke so, idan sun karbi mulki kuma za su gallaza wa ‘yan Arewa ne, amma idan ya koma kan kujera cikin yardar Allah abubuwan gaba daya Allah za su warware. Duk inda aka samu akasi, Buhari zai gane zai yi kokari a gyara, domin tallafin da akace an cicciren nan an kara kudin mai domin a samu hanyar kudin shiga domin a juya a waiwaiyi talaka. An kara kudin shiga domin a taimaki talaka ne, to idan aka ce an tara kudin nan Buhari ya zo bai koma kan mulki ba, me akayi?

Ya tara a 1983-5 Buhari ya Tara wa kasar nan kudi, amma abin da ake son aka yi kudin bai yiwu ba, ya bar kujerar, yanzu kuma bayan shekara 30 Allah ya sake ba shi mulki ya zo ya sake tara kudi, ana fama akawar da shi, yana ji yana gani za a cutar da inda yake da inda yake tinkaho da ita, wato Arewa, mutumin Kudu ba ruwansa da kana kirista ko kana musulmi, in dai kai dan Arewa ne, shi ke nan.

Ya kamata Buhari ya fahinci cewa Allah na ganinsa ya fa rantse da Kur’ani ya yi alkawari zai yi adalci zai taimaka wa talakawa, talakawa na cikin wahala, mu muka zabe shi, muna tare da shi, ba za mu ja da baya ba. Shi ya sa muke bukatar ya dawo kan kujerar nan, akwai danmu, wanmu, uba wanda yake neman wannan kujera, shi ne Wazirin Adamawa, amma muka a jiye batunsa. To Buhari ya kamata ya duba ya kawo wa talaka saukin rayuwa. Za mu ci gaba a mako mai zuwa.

 
Advertisement

labarai