Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta amince da kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa, wadda za ta kasance cibiyar farko irinta da wata jami’a za ta kafa a Nijeriya.
An cimma wannan matsaya ne a taron Majalisar Zartarwar Jami’ar na 429, da aka gudanar a ranar Laraba, 29 ga Oktoba, 2025, a wani bangare na ƙoƙarin jami’ar na inganta ilimin aikin jarida da kuma tunkarar manyan sauye-sauyen da ke faruwa cikin sauri a fagen sadarwa.
- Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya
- Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70
Tuni an samar da kudaden da za a yi amfani da su wajen fara kafa cibiyar, wadda za ta mayar da hankali kan shirye-shiryen digiri na biyu da na uku, horaswar aiki ta zahiri, gudanar da bincike, da kuma haɓaka haɗin gwiwa da masana’antar kafofin watsa labarai. Babbar manufarta ita ce cike gibi tsakanin darussan da ake koyarwa a aji da kuma yadda ake aiwatar da su a wajen aiki, tare da tallafa wa ‘yan jarida da masu bincike su samu cikakken ilimi da kwarewar da ta dace da zamanin dijital.
A cewar Majalisar Gudanarwar Jami’ar, kafa cibiyar na da alaƙa da fahimtar irin sauyin da kafafen watsa labarai na duniya ke yi da kuma bukatar zurfafa bincike a fannin aikin jarida, sababbin fasahohi, da labarai na dijital. Da zarar cibiyar ta fara aiki, ana sa ran za ta ƙara tabbatar da matsayin BUK a matsayin jagora a fannin ilimin jarida da sabbin kirkire-kirkire a Nijeriya.
Jami’ar ta bayyana wannan mataki a matsayin wani mahimmin ci gaba da ya yi daidai da manufarta ta bunƙasa bincike, haɓaka kirkira, da gina ƙwararrun masana.
An fara koyar da aikin jarida a Nijeriya tun farkon bayan samun ‘yancin kai, kuma BUK ta kasance cikin jami’o’in farko da suka kafa sashen Koyar da Aikin Jarida (Mass Communication). A tsawon shekaru, jami’ar ta samar da fitattun ‘yan jarida, malamai, da ƙwararrun ma’aikatan kafofin watsa labarai da ke taka rawa a fadin ƙasar.
An gina ra’ayin kafa wannan cibiyar ne a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Umaru A. Pate, shahararren masani a fannin jarida kuma jajirtaccen mai fafutukar gyaran tsarin kafafen yaɗa labarai a ƙasa. Hangen nesa da shawarwarinsa sun taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa madogarar bincike da ci gaban ilimin jarida a BUK.
Da zarar an kammala cikakken kafuwar cibiyar, ana sa ran za ta ƙara ɗaukaka sunan Jami’ar Bayero Kano, tare da ƙarfafa matsayinta a matsayin cibiyar ƙwarewa, kirkira, da bin ka’idojin aikin jarida na gaskiya da rikon amana.













