Daga Lawal Umar Tilde, Jos
Kasa da ‘yan makonni kali’lan a gudanar da zaben kana’nan hukumomi a jihar Filato, an bukaci gwamnan jihar Barista Simon Bako Lalong, da ya yi sauye-sauyen mukamai a gwamnatinsa.
Wani jigo a siyasar jihar mai suna Alhaji Danlami Abubakar ne ya nuna bukatar haka yayin wata ganawa da LEADERSHIP A YAU ta yi da shi kwanan nan a Jos babban birnin jihar.
A cewar Abubakar, ya zama wajibi ga gwamnan da ya yi sauye-sauye a jam’iyyar don ta sami zarafin taka kyakkyawar rawa a zaben kananan hukumomi da ke tafe da ma zabubbukan 2019.
Ya ce gwamna ya sami nasarori masu dimbin yawa tun hawansa karagar mulkin jihar a 2015 da suka hada da maido da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’ummar jihar, biyan basussukan albashin ma’aikata da fansho wanda ya gada daga tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta PDP, da kuma karasa gyra hanyoyi da biyan ‘yan kwangila basussukan da suke bin gwamnati.
Alhaji Abubakar ya yi amfani da wannan dama wajen mika rokonsa ga al’ummar jihar da su kara bai wa gwamnan goyon baya da hadin kai don ya sami sukunin gudanar da dimbin ayyukan inganta rayuwar al’umma da yake kokarin aiwatarwa wadanda suka hada da gyran hanyoyin cikin garin Jos da na karkara da za su hade hedkwatocin kananan hukumomi 17 da Jos babban birnin jihar da gina babbar kasuwar Jos kamar yadda ya sanar wa al’ummar jihar a jawabinsa na farkon kama aiki.