An Bukaci Gwamna Lalong Ya Yi Sauye-Sauyen Shugabannin Siyasa

Daga Lawal Umar Tilde Jos

Kasa da yan makonni kali’lan a gudanarda zaben kana’nan hukumomi a jihar Filato, an bukaci Gwamnan jihar Barista Simon Bako Lalong, da ya yi sauye- sauyen makaman shugabannin da su ke rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa.

Daya daga cikin magoya bayan jam’iyyar APC, a cikin garin Jos fadar gwamnatin jihar Alhaji Danlami Muhammed ne, ya yi wannan kira alokacin da yake tattaunawa da Jaridar LeadershipA Yau, a makon nan da ya gabata.Yace ya zama wajibi wa gwamna da yayi sauye -sauye a jam’iyyar don ta sami taka kyakkyawar rawa a zaben kana’nan hukumomi dake tafe da zabubbuka masu zuwa a 2019.

Alhaji Muhammed, wanda ya yaba bisa dimbin nasarorin da gwamnan ya samu a cikin shekaru biyu din da ya’yi da kama ragamar mulkin jihar, ya nuna jin takaicinsa bisa ganin da yawa daga cikin wadannan shugabannin saboda son kai da rashin kishi yasa sun kasa gudanarda harkokin jam’iyyar a yankunansu.Ya ce misali, a karamar hukumar Jos ta Arewa da take cibiyar gwamnatin jihar, mutum zai iya zaga dukkan unguwannin ba zai ga Tutar Jam’iyyar APC ba da za ta nuna wannan ofishin ja’iyyar balatana ya ce zai iya kai koke ko shawara.

Yace gwamna ya sami nasarori masu dimbin yawa tun hawansa karagar mulkin jihar a 2015, wanda yace, sun hada da maido da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’ummar jihar, biyan basussukan kudaden Albashi da na Fensho da ma’aikata ke bin bashi wanda yagada daga tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta PDP, da karasa gyara hanyo’yi da biyan ’yan kwangila basussukan da suke bin gwamnati.

Alhaji Muhammed, ya roki al’ummar jihar da su kara ba gwamnan goyon baya da hadin kai don ya sami sukunin gudanarda dimbin ayyukan inganta rayuwar al’umma da yake kokarin aiwatarwa wadanda suka hada da gyran hanyoyi cikin garin Jos da na karkara da za su hade hedkwatocin kana’nan hukumomi 17  da Jos babban birnin jihar da gina babbar kasuwar Jos kamar yadda ya sanar wa al’ummar jihar a jawabinsa na farkon kama aiki.

Hukumar farfado da abinci ta hanyar ayyukan noma waddda ke karkashin majalisar dunkin duniya da aka fi sani da Food Agricultural Organisation (FAO) ta raba awaki 3,600 ga mata 900, wadanda suka rasa mazajen su ta dalilin tashin-tashinar Boko Haram a Maiduguri, da nufin bunkasa yanayin rayuwar su.

Babban jami’i mai kula da wannan hukumar Mista Musa Kida ne ya bayyana hakan ga manema labarai a sa’ilin da yake kaddamar da raba garken awakin ga ayarin matan a yankin Memusari dake kwaryar babban birnin jihar, Maiduguri.

“Mun tsara wannan tallafin namu kaso biyu ga bangaren mata, musamman wadanda suka rasa mazajen su ta dalilin matsalar rikicin Boko Haram; yayin da a kwanan baya muka fara da raba musu kayan noma domin wannan damina ta bana, sai kuma na yanzu wanda muke raba musu awakin kiwo”. In ji shi.

“Muna kyautata zaton wadanda suka ci gajiyar wadannan dabbobin kan su yi kyakkyawan tanadin su domin bunkasa yanayin kiwon inda hakan zai taimaka wajen dogaro da kai da bunkasar tattalin arziki da zai rage dawainiyar yau da kullum”.

Haka zalika kuma, kowacce mace daya ta samu awaki hudu. Sannan ya sake bayyana cewa” kawowa yanzu, mun tsara cewa yankuna 17 ne zasu ci gajiyar wannan tallafi; yanzu mun fara da Jere da kuma cikin Maiduguri. Baya ga wannan kuma zamu zakuda zuwa garuruwan Zabarmari da Gongula da kuma Dusuman.

Musa Kida ya tabbatar da cewa, ko shakka babu wannan tallafin bada cikakkiyar ma’ana ga rayuwar wadanda suka ci gajiyar sa sannan kuma ya taimaki rayuwar su.

Bugu da kari kuma, shugaban hukumar ya nanata cewa yanzu haka kimanin mata manoma 4,000 ne suka amfana da tallafin noman da wannan hukuma ta su ba mata a jihar a farkon daminar Bana.

Leadership A Yau ta zanta da daya daga cikin matan da suka ci gajiyar wannan taklafi na FAO, malama Fatima Musa inda ta bayyana gidiyar ta, kana ta sha alwashin tanadin wadannan dabbobin.

Fatima ta shaidar da cewa, wannan tallafin zai taimake ta wajen samun abin dogaro da kai. Inda ta kada baki ta ce “Ina da yara biyu wadanda mijina ya bari; yan kugiyar Boko Haram ne suka kashe shi, haka siddan. Gaskiya mun ji dadin wannan taimakon kwarai kuwa”. In ji ta.

Exit mobile version