Bukatar A Dakile Matsalar Wutar Lantarki

Matsalar wutar lantarki ba sabon abu ba ne ga Dan Nijeriya tun a zamanin gwamnatocin baya har kawo yau. Al’ummar kasar ta riga ta saba, masu kayan sana’a da lantarki sun nemi kananan injinan lantarki domin tsaron lalurar daukewar wuta. Hamshakai masu kwana da na’urorin sanyaya daki lokacin zafi ko zafafawa a lokacin dari sun kasa rayuwa a Nijeriya face da injin samar musu da lantarki a iya yankin gidajensu. Don haka matsalar ba bakuwar aba ba ce ga ko wane mataki na ‘Yan Nijeriya. Bakon abu a wurinsu shi ne yaushe za a yi ban-kwana da matsalar?

A kwanan baya, wata hukuma mai auna yanayin karfin lantarkin kasashen duniya ya ayyana Nijeriya a matsayin kasa ta biyu mafi matsalar wutar lantarki a duniya a shekarar 2017. Matsalar ta zama karfen kafa ce saboda irin yadda gwamnatocin baya suka kashe zunzurutun kudi sama da Naira tirilyan biyu daga shekarar 1999 zuwa 2015 da nufin samar da sahihiyar wutar lantarki a kasar, amma abin ya faskara duk da cewa ana ganin bude kofar da gwamnati ta yi a kan masu zuba jari su shigo ciki ba karamar farar dabara ba ce.

A lokacin da Nijeriya ta samu nasarar samar da karfin wuta megawatt 5,074, ko wane dankasa nagari ya tabbatar da cewa an kama kwakkwarar hanyar magance matsalar saboda kafin lokacin, ba a taba samun karfin wutar ya wuce megawatt dubu hudu da ‘yan kai ba.

Masana lantarki sun ce akalla Nijeriya tana bukatar amfani da wuta megawatt 160,000 a cikin gida kawai. Amma kuma ta yaya za a cimma haka alhali a watan Oktoban 2017, an ruwaito ministan lantarki Fashola yana cewa idan an hada dukkan wutar da manyan tashoshin samar da lantarki na ruwa da ke Ka’inji, Jebba da Shiroro ke samarwa, du-du-du ba ta wuce kashi 25 a cikin 100 ba. Wannan ya nuna an samu karin kashi 15 a cikin 100 daga shekarar 2015, inda bangaren gas kuma ya kwashi kashi 74 a cikin 100. To, ina ma a ce hakan zai rika karuwa sannu-a-hankali?

Wani rahoto da aka fitar kwanan nan ya nunar da cewa Nijeriya yanzu haka tana samun wuta megawatt 4,000. Rahoton ya bayyana cewa sai dai wani lokaci kamar a wannan watan na Janairu abin ya dan sauka kadan da megawatt 168 da ‘yan kai. Da yawa, masana na ganin abin da Nijeriyar ta dogara da shi wurin samun hasken lantarki tsohon yayi ne da ya shafe sama da shekara 45 ana amfani da shi, wato ruwa da mai da gas da kwal. Baya ga tsofewar hanyoyin, har ila yau ko wanne yana da nashi matsalar da ke neman kassara shi.

Domin lalubo bakin zaren warware matsalar, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta yi tunanin samar da wutar lantarki ta wasu makamashin da ba wadannan da muka lissafa ba. Duk wata maganar da za a yi ta bunkasa tattalin arzikin kasa za ta zama an-gudu-ba-a-tsira ba, matukar babu isasshiyar wutar lantarki. Komai kwazon mutum da son sana’arsa, da zarar an dauke wuta ba shi da injin samar da lantarki sai dai ya rungume hannu ya yi kallo.

Kasar da take fama da rashin kayan more rayuwa, makamashi na tsohon yayi, karancin kudin shiga, satar kayan lantarki da rashin biyan kudin wuta, zai yi mata wuyar gaske ta samu biyan bukata kan abin da take so kamar yadda ya kamata.

Saboda haka, rayuwar Nijeriya za ta cigaba da bundun-bundun matukar gwamnati ba ta shawo kan matsalar lantarki ba.

Hanyoyin da kasar za ta bi kuwa su ne, ta binciko gafiyoyin da suka yi sama-da-fadi da kudin lantarki a hukunta su dai-dai da barnar da suka yi na tadiye kasa.

Bangaren na lantarki ya sha sauye-sauye da dama, tun daga kan hukumar da ke samar da wutar har zuwa kan yadda aka fasalta mallaka wa ‘yankasuwa lamarin. Masu zuba jarin sun zo, sun shiga ana damawa da su amma har yau matsalar ba ta kau ba.

Sannan galibin hukumomin da suke rarraba wutar lantarkin sun dukufa ga neman cin riba ta ko wace fuska maimakon gyara tukuna. Har ma a kwanan baya ministan lantarki Fashola ya ce Nijeriya ba ta da isasshen kayan aikin da za su iya daukar lantarki mai karfi sosai.

Tabarbarewar da wutar lantarkin kasar nan ya yi, yana daga cikin manyan ginshikan da suke dankwafar da Nijeriya tare da hana mata cigaban tattalin arziki. Bayan haka, duk da zunzurutun kudin da aka narka domin gyara sashen wutar lantarkin abin ya faskara, sai dai a fice daga wannan matsalar zuwa wancan, ‘Yan Nijeriya har sun gaji sun zuba ido. Fatanmu Nijeriya ta yi sallama da duhu, haske ya zauna.

 

Exit mobile version