Nasir S Gwangwazo" />

Bukatar Fifita Masana’antun Kera Motocin Gida Nijeriya

A umarnin da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayar a kwanan nan ya bukaci ’yan Nijeriya su fifita masana’antun kera motoci na cikin gida. Haka nan majalisar Jihar Anambra ta gabatar da kudirin yin watsi da amfani da motaci kirar Toyota Prado Jeeps, wanda fadar gwamnatin jihar ta bayyana aniyarta ta saya mu su, ta na mai cewa, cigaba da amfani da motocin zai hana bunkasa masana’antar kira motoci ta Innoson Jeeps.

A cikin shekarar 2016, gwamnatin tarayya ta umarci ma’aikatun gwamnatin tarayya da su fifita masana’antun kera motocin gida Nijeriya wajen yin amfani da motocin da su ke bukata.

Shugaban kasa ya bayar da wannan umarni ne lokacin da ya ke kaddamar da motoci guda 283 kirar gida, wadanda a ka saya wa hukumar kiyaye hadararruka ta kasa, domin su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Motocin, wadanda su ka hada da motar sintiri, bas din bayar da agaji da kuma tirelar jan motoci, wanda kamfanin Peugeot Automobile Nigeria Limited da masana’antar kira motoci ta Innoson Behicle Manufacturing Company Limited da kuma kamfanin Nissan Nigeria, su ka samar ne.

Hakazalika, a cikin watan Junairun shekarar 2018 ne rundunar sojin Nijeriya ta fara amfani da motoci kirar kamfanin Innoson Motor Manufacturing Company, wadanda a ka bai wa rundunar Operation Lafiya Dole da kuma wasu rundunonin sojoji masu gudanar da sintiri.

A watan Afrilun shekarar 2019, gwamnatin tarayya karkashin wannan tsarin ta saya wa hukumar kiyaye hadararruka ta kasa sababbin motocin sintiri guda 77, domin su tabbatar da tsaron ‘yan kasar nan. Motocin dai wadanda a ka saya daga kamfanin Innoson sun hada da, IBM 4D2 budaddu guda 77 da kuma motocin daukar marasa lafiya guda uku.

‘Yan majalisar Jihar Anambra, sun bayyana cewa, cire kudi har naira biliyan daya domin sayan motoci kirar Toyota Prado Jeep, wani bannan kudi ne, domi za a iya samun irin wadannan motoci  a kamfaninn Innoson Motors Limited da ke jihar cikin farashi kasa da haka. Inda su ka bayyana cewa, kamfanin ya na daukar matasa aiki, sannan kuma ya na biyan gwamnati haraji. A cewar ‘yan majalisun, gwamnatin Jihar Anambra tare da sauran gwamnonin jihohin kudu maso gabas da kudu maso kudu sun dade su na tallata masana’antu da ke kera motoci a Nijeriya. Babu wani dalili da ba za a tallata masana’antun kera motocin gida. Su na kera su ne da karafunan gida Nijeriya. Su na da saukin kulawa sannan kuma za a iya samun su a ko’ina a kasar nan. Ya na da matukar muhimmanci tallata kamfanonin kera motocin gida, domin su na samar da ayyukan yi ga matasa.

Har ila yau, ra’ayinmu shi ne, ya na da kyau a tallata masana’antun kera motoci a Nijeriya, domin a zahirin ma ya na inganta bunkasa fasaha ga ‘yan Nijeriya, amma ya na da kyau a yi hadin giwa da wasu masana daga kasashen waje. Mu na kokarin bayar da gudunmuwa ga masana’antun kera motocin gida, amma mun kasa shawo matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yamma. Shekaru uku kenan da rundunar sojojin saman Nijeriya, ta bayyana cewa, za ta hada giwa da kamfanin kera motoci na Innoson Behicle Manufacturing, domin kamfanin ya samar da sassan jirgin yaki wajen dakile rashin tsaro. Sai dai kamfanin ya gaza cigaba da samar da kayan aikin yin jirgin yakin. Kamfanin ya gaza ne sakamakon bai samu wani taimako daga waje ba. A shekarar 2015, rundunar sojojin saman Nijeriya ta bayyana cewa, kamfanin Innoson ya gaza samar da sassan karafan jingin yakin. Haka nan wannan lamarin ya rushe sakamakon rashin jawo ‘yan kasar waje.

Rufe iyakokin Nijeriya da a ka yi a kwanan nan, wanda masu ruwa da tsaki su ka yaba da tsarin hana shigowa da shinkafar waje da wasu abubuwan da a ka hana shigowa da su, kamar su motoci, domin karfafa wa manoma da masana’antu kwarin giwar bunkasa tattalin arzikin kasar nan. An ce sai ‘yan Nijeriya sun sayi shinkafar gida, sannan kuma jami’an gwamnati su na tuka motocin kasar waje. Da wannan ne mu ke bayar da shawara a kan dukkan motocin jami’an gwamnati ya zama an saye su ne daga kamfanin kera motocin gida Nijeriya. Wannan zai bunkasa tattalin arzikin kasar nan da samar wa matsa ayyukan yi da kuma rage amfani da kayayyakin kasar waje.

Da haka ne mu ke yaba wa ‘yan majalisar Jihar Anambra, a kan tallata masana’antar kera mota na gida, wajen shirin bai wa gwannatin jihar shawaran yin amfani da motocin kirar Toyota Prado Jeep kirar gida da kuma yin watsi da amfani da motoci kirar Toyota Prado Jeeep na waje.

Ya kamata sauran jami’an gwamnati su yi koyi da ‘yan majalisar Jihar Anambra. Mun sani cewa, majalisar kasa ta ware kudade hai naira biliyan 5.5, domin sayan ma ‘yan majilisa motoci. Mu na kira a gare su da su yi amfani da wadannan kudade wajen tallata masana’antar kera motocin gida Nijeriya, indai har su na son cigaban kasar nan. Indai majalisar kasa ta saka wannan kudade ga hannun kamfanonin kera motocin gida, to tabbas zai taimaka wa kasar ta hanyoyi da dama.

Exit mobile version