Nasir S Gwangwazo" />

Bukatar Gudanar Da Zaben Jihohin Kogi Da Bayelsa Cikin Lumana

Kowacce kasa ta duniya da ke bin mulkin dimokradiyya ta na bukatar gudanar da sahihin zabe. Haka lamarin ya ke a Nijeriya. Wannan ne ya sa tashin hankali ba shi da wajen zama a duk kasashen da ke aiwatar da tsarin dimukradiyya.

Kowacce al’umma ba ta bukatar tashin hankali a wajen gudanar da zabbuka, domin haka ne ma jam’iyya mai mulki, APC, da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Nijeriya su ka yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su kauce wa duk wani lamari wanda zai kawo tashin hankali a zaben gwamna na jihohin Kogi da Bayelsa.

A makon da ya gabata ne, jam’iyyar APC ta zargi jam’iyyar adawa da yunkurin kawo tashin hankali a zabukan gwamnoni da za a yi ranar 16 ga Nuwamba, 2019, a cikin wadannan jihohi guda biyu. Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC, Malam Issa-Onilu, ya bayyana cewa, ya samu labarin cewa, PDP ta na shirin sayen kuri’u da kuma kokarin tayar da hargitsi zabe a Jihar Bayelsa.

Samun wannan zargi ke da wuya, nan ta ke PDP ta mai da martani, inda ta ce, jam’iyya mai mulki ta bayyana abinda ta ke so ta aiwatar a kan ‘ya’yan PDP na tashin hankali a lokacin wannan zabe ne; shi ya sa ta fara dora wa jam’iyyun adawa laifi.

Babu shakka an shirya makarkashiya a wadannan zabe da za a yi cikin jihohin nan guda biyu. Babu shakka wadannan manyan jam’iyyun siyasa guda biyu sun shirya bin duk wata hanya da za ta sa su yi nasara a wadannan zabubbuka.

Abin farin cikin shi ne, hukumar zabe mai zaman kanta ta hada kai da jami’an tsaron kasar wajen tsaurara matakan tsaro a jihohin Kogi da Bayelsa, saboda wannan zabe mai zuwa, domin wadannan jihohi guda biyu su na da tarihin tashin hankali wajen gudanar da zabe.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce, hukumarsa tare da jami’an tsaro za su dauki matakan da su ka dace a wajen gudanar da zabubbukan. Ya kara da cewa, an taba samun tashin hankali a wadannan jihohi a zabukan da su ka gabata. Ya ce, an samu bayanai da ke nuna cewa, an yi hayar ‘yan dabar siyasa na cikin gida da na waje, domin su tarwatsa wannan zabe.

’Yan sanda sun shirya tsaf wajen dakile duk wani lamari da zai kawo wa zaben cikas. Rundunar ‘yan sandar Nijeriya, wacce ta ke da alhakkin kawo tsaro, ta bayyana cewa, ta girke jami’anta guda 66,241 tare da wasu jami’ai na musamman guda 31,041 wadanda za su yi sintiri lokacin gudanar da zaben a Jihar Bayelsa. Haka kuma ta girke jami’anta guda 35,200 a jihar Kogi.

Wadannan jami’ai dai aikinsu shi ne, su tabbatar da tsaron rayukan matane tare da kayayyakin zabe, domin a tabbatar an yi zabe cikin kwanciyar hankali. Za a samu jami’an tsaro a dukkan mazabu tare da kuma ma’aikatan zabe a kowani wurin amsar sakamako.

Babban mai ba wa shugaban kasa shawara ta harkar tsaro, Babagana Monguno,  shi ma ya tofa albarkacin bakinsa a kan wannan zabe da za a yi a jihohin nan guda biyu. Ya bayyana cewa, an saba samun tashin hankali a duk lokacin da a ke gudanar da zabe a jihojin Bayelsa da Kogi, domin haka ne ya shawarci ‘yan siyasa da su guji tayar da hankali, domin an girke jami’an tsaro wadanda za su fuskanci duk wanda ya yi yunkurin kawo rikici lokacin zabubbukan.

A wannan jaridar, mun yaba wa jami’an ‘yan sanda wajen girke takaru masu yawa domin kawo tsaro lokacin wannan zabe. Amma kuma duk da haka ba ya nuna cewa ba a samu wani tashin hankali ba. A wasu lokutan, jami’an tsaro su ke haddasa tashin hankali wajen gudanar da zabe.

A wannan lokaci, ya kamata rundunar ‘yan sanda ta ja kunnen jami’anta a kan duk wani jami’i da a ka samu ya na da hannu wajen yin magudin zabe ko kuntata wa mutane ko kuma sakaci da aiki, to zai fuskanci mummunan hukunci.

An girke su ne domin su gudanar da aiki yadda ya kamata, ba don su samu kudi ba ta haramtacciyar hanya.

Ya kamata ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro su dakile shigo da makamai a wadannan jihohi guda biyu, wanda a ke bai wa ‘yan daba domin a yi amfani da su wajen jin zabe. Mu na da tabbacin cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta shirya tsaf, domin gudanar da sahihin zabe.

Dole hukumar zabe mai zaman kanta da jami’an tsaro su yi aiki tare wajen tabbatar da dakile ayyukan gurbatattun ‘yan siyasa da ‘yan dabansu wadanda ke kokarin tarwatsa zabe a cikin wadannan jihohi guda biyu. Ya kamata a dauki darasi a kan tashin hankalin da a ka samu a babban zabe, domin kauce wa faruwar irin wannan lamari a zabubbukan.

Exit mobile version