Bello Hamza" />

Bukatar Hadin Kai Tsakanin Shugaba Buhari Da Majalisa Don Ci Gaban Kasa

Daga Bello Hamza

A halin yanzu zaman doya da manjan da ake yi tsakanin ofishin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Majalisar Dokoki ta tarayya ba wani abu daya zama sirri bane, al’amarin ya kai kamarin da kwanakin baya shugaba Buhari a wani jawabi daya gabatar ya dora alhakin tafiyar hawainiyar da gwamnatinsa ke yi wajen aiwatar da mahimman aiyyuka a kan rashin samun hadin kai daga majalisar tarayya wajen amincewa da kudurorin da gwamnatinsa ke aikawa domin samun amincewar majalisar tarayya.

Nan da nan Shugaban Majalisar Dattijai Dakta Bukola Saraki ya karyata zargin daya fito daga fatar Shugaban kasar ya na mai cewa,  a cikin shekara 3 da ake ciki na wannan zangon mulkin dimokradiyyar da shugaba Buhari ke jagoranta fadar Shugaba Buhari ta turo wa majalisa mutum 227 da aka turo daga fadar shugaban kasa domin amincewa dasu a kan mukamai daban-daban a cikin su mutum 133 kawai ne majalisar ta ki amincewa da su. Cikin wadanda aka fi cecekuce daga wadanda majalisar ta ki amincewa dasu a kwai shugaban Hukumar EFCC, duk da kundin tsarin mulkin kasar nan ya ba majalisar karfin amincewa da kin amincewa da wanda fadar shugaban kasa ta turo domin a tabbatar da shi a kan zama wani mukami, a kan batun Ibrahim Magu sau uku fadar shugaban kasar ke mika sunansa kuma sau uku kuma majalisar dokoki na kin amincewa da shi, cikin hujjojin da majalisar ta dogara dasu wajen kin amincewa da Magu, ya hada da rahoton da hukumar leken asiri ta DSS ta bayar a kan wasu badakalar da Ibrahim Magu ke da hannu a ciki, masana na da ra’ayin cewa, rashin amincewa da Magu a matsayin shugaban na EFCC ya taka muhimmiyar rawa wajen rage karfin aikinsa na yaki da cin hanci da rashawa, abin da ake gani a matsayin babban alkawarin da wannan gwamnatin ta yi wa mutanen Nijeriya lokacin yakin ta na neman zabe.

Rashin amincewa da majalisar ta ki yi wa wasu da fadar gwamnatin Buhari ta miko mata har ya samu tsokaci daga wasu hukumomi na kasashen waje ciki kuwa har da Hukumar Lamuni ta Duniya “IMF”, in da a kwanaki ta yi kira na musamman ga jagororin majalisar kasa da su gaggauta amincewa da manbobin hukumar gudanarwa na babban bankin kasa (Central Bank of  Nigeria) da kuma hukumar harkar tsare-tsaren kudi na kasa “Monetary Policy Committee, MPC”, saboda a samu karfin fusakantar farfado da komatsar tattalin arzikin kasar nan da ke fitowa daga durkushewar da ta yi a ‘yan shekarun nan, su na masu lura da cewa, rashin hukumar gudanarwa a wadannan muhimman hukumomin kudi na gwamnati ba zai haifar wa da kasar nan da mai ido ba a hankoronta na ci gaba da zama cikin kasashe masu samun bunkasar tatalin arziki a duniya.

A lokacin da takadamar amincewa da Ibrahim Magu a matsayin shugaban Hukumar EFCC ya sake tasowa a farkon wannan shekara masana sun bukaci fadar shugaban kasa ta garzaya babban kotun koli domin neman fassarar sashi na 171 na kundin tsarin mulkin shekara 1999, sashin dai ya tattauna ne a kan nau’in ma’aikatan da fadar shugaban kasa ke bukatar amincewar majalisar dattijai kafin a nada su maimakon takaddamar da ake ta yi a kan amincewa ko rashin amincewa da Ibrahim Magu a matsayin shugaban Hukumar EFCC, kotun koli ne kwai za ta raba gardama a kan wanene ke a kan gaskiya, hakan kuma ne kawai zai taimaka a samu ci gaba a yakin da ake da cin hanci da rasahawa a kasar nan.

A ‘yan kwanakin nan an samu zazzafan takaddama tsakanin majalisa da wasu hukumomin gwamnati wannada hakan ya na kawo cikas wajen gudanar da aiyyukan yau da kullum na ci gaban alumma, shugaban majalisar Datijjai Bukola Saraki ya zargi hukumomi da ma’iakatun gwamnatin tarayya da kin bayar da hadin kai wajen mika kundin kasafin kudinsu na wannan shekarar duk da wa’adin yin haka da majalisar ta basu har sau biyu, a bin da ke haifar da tsakon da ake fusakanta na rashin zastar da kasafin kudin wannan shekara har zuwa yanzu, wannan rashin hadin kan babban matsala ne ga harkar tafiyar da mulki, a nan ma ya kamata fadar shugaban kasa ta yi gaggawar shigo wa domin ganin hukumomi da ma’aikatunta sun bayar da cikkaken hadin kai domin ganin an samu zastar da kasafin kudin wannan shekarar cikin lokacin daya kamata.

Takaddama na baya-bayan tsakanin bangaren zastarwa da bangaren majalisar tarayya shi ne na jadawalin zabe da hukumar INEC ta tsara, majalisar dattijai kuma ta yi wa kwaskwarima, hakan ya tayar da jijiyar wuya tsakanin ‘yan majalisa da ake ganin masu goyon bayan fadar shugaban kasa ne da wadanda a ke ganin masu goyon bayan shugaban majalisar dattijai ne, wannan takaddama yana iya kawo barazana da cikas ga shirye-shiryen da ake yi na gudanar da zaben shekara mai zuwa na 2019, a kwai misalai da dama na matsaloli da rashin jituwa da ake fuskanta tsakanin majalisar kasa da fadar shugaban kasa, wanda hakan babban barazana ne ga mulkin dimokradiyyamu.

Duk lokacin da bangaren zartasawa da na dokoki suka shiga takaddama tsakaninsu harkar gudanar da gwamnati ne ke fuskantar baraza, ci gaban tattalin arziki da gudanar da aiyyukan da zai taimaki rayuwar dimbin alummar kasar nan ya kan shiga cin matsala, abin da kan shafi romon dimokradiyyar da alumma ke fatan samu, abin lura anan shi ne a tsarin mulkin shugaba mai cikkaken iko, ko wanne bangare na da karfi da iko da tsarin mulki ya ba shi kuma dole kowanne bangare ya mutunta daya bangaren, ta haka ne kawai za a samu fahintar juna, a kwai bukatar jagororin majalisar kasa da na bangaren shugaban kasa su dare teburin tataunawa domin gano bakin zaren, su kuma bude babin fahintar juna tsakaninsu domin gudanar da aiyyukan da zai ciyar da alummar kasar gaba, duk kuma lokacin da aka samu wani rashin fahinta sai a mika matsalar ga bangaren shari’a domin sun ne doka ta ba aikin fassara da karin bayani a kan matsalar daya shiga duhu a wajen gudanar da tadane-tanaden da ke cikin tsarin mulkin kasar nan. Abin mamaki da takaici a wannan takadadamar da ke faruwa tsakanin ofishin shugaban kasa da na majalisar tarayya shi ne dukkan bangarorin jam’iyya daya wato APC ke jagorantar su, saboda haka a kwai bukatar jamiyyar ta yi gaggawar shiga cikin matsalar domin gano hanyar kawo fahintar juna tsakanin fadar shugaban kasa da bangaren majalisar dokoki domin kawo ci gaban kasa da tabbatauwar mulkin dimokradiyya.

Exit mobile version