Connect with us

LABARAI

Bukatar Jam’iyyun Siyasa Su Kai Zuciya Nesa

Published

on

Kwanci tashi babu wata wuya wurin Allah sai ga shi cikin ikon Allah da kuma yardarm ta shi, zamu sake ganin zaben fidda gwani wanda jam’iyyun siyasa suke yi, saboda su fitar da dan takarar da suke ganin zai iya fafatawa da sauran abokan da suke neman ita jam’iyyar ta su ta tsayar da shi a matsayin dan takararta. Hakika ko shakka babu wannan ba karamin aiki ne ga tun daga su wadanda suke bukatar jam’iyyun nasu su tsayar dasu a matsayin ‘yan takara , da wadanda wakilan jam’iyyun wadanda ake kira da suna delegate wato wakilai zasu zabe su, wasu jam’iyyun su kan yi amfani da hanyar zabe ta ‘yartinke, wanda sau da yawa  dantakara yana iya gane ko zai kai gaci ko kuma ba zai kai ba, wato lokacin da yaga dogon layin mutanen da suke goyon bayan shi ko kuma wani abokin adawar sa. Yayin da kuma wasu jam’iyyun siyasar zabcen ‘yan takarar na sirri ne suke yi  saboda koma dai me zai iya faruwa daga baya, ko ka zabi wanda yake sa ran zai samu kuri’arka ko baka zabe shi ba, ba zai iya sani ba. Sabanin shirin zaben ‘yartinke wanda mutum yana ji yana gani zai ga wanda ke kaunar sa da kuma wanda bai kaunar shi. Zaben fitar da gwani jam’iyyun siyasa, da kuma ‘yantakara duk sun kasance Dan jummai da Jume da kuma Jummai ko kuma Jummala saboda ai duk ‘yan uwan juna ne amma dai halayyarsu ce ana iya cewa ta dan shan bamban .

Tun ma kafin ayi nisa sai an tada gizo sannan ace koki ta taso, idan muka fara da ‘yansiyasa ba muyi ma kowa laifoi ba, sune suke tsayawa takara saboda cikin su ake samun wadanda suke sha’awar tsayawa takara da kuma bazarsu ita jam’iyyar siyasar taka rawa. Ashe wannan ya nuna  kowa ya san abinda zai iya da kuma wanda yafi krfin shi,kamata ya yi abinda zai iya kwashewa da maraba  wai don kawai ya burge mutane ba, ba maganar karya, ko abinci ma mutum ya san irin wanda zai iya cinyewa shi kadai. Idan mutum shi Kansila yake da karfin yi to ya tsaya a can kar ya ce, sai  ya fito takarar majalisar jihar, wanda kuma yake da karfin na jiharn kar ya ce, sai ya tsaya dan majalisar wakilar ta tarayya, kai haka dai abin yake  tafiya har sai an kai ga kujerar shugaban kasa. Ba kuma sai an tura kaba ko an fada maka kai da kanka ka san abinda zaka iya da kuma wanda ba zaka iya ba, idan kai tunani wannan magana gaskiya ce.Ka rabu da duk wanda ko wadanda zasu iya ma iza mai kantu ruwa, shi ko kuma su akwai abin ko kuma abubuwan da suka ganio tattare da kai, watakila ko wani maski maski suke ganin kana yi, saboda mai hannu da maski shi ake ba murzar zare. Idan kuma basu gani ba ai ba zasu ce da kai hakan ba. Saboda haka ba sai an ce ma komai ba, akwai kujeru daban daban tun daga ta Kansila zuwa Shugaban kasa, inda ake samun matsalar shi ne, kai baka kai ga sumar wasu ba sai k ace zaka yi askin wasu. Ya kamata ka yi tunani kai ka san kan ka fiye da kowa, ba sai an fada ma cewar kai ne wane ba, rabu da masu cewar sai ka yi bayan kai kuma ka san ba zaka iya ba, koda kuwa a faranti aka zuba bayan kasawar , kai da kan ka, ka san, wani abin yafi karfin ka, ko kuma ka kwashe shi idan ma ya kasance kayan da za a dauka, ba ace ba zaka fara  ci ba, wannan gaskiya ne zaka fara ci.  Eh zaka fara cin amma ba zaka iya cinyewa ba watakila sai ma ka nemiabokin da zai taimaka maka. Kar ka yaudari kan ka ko kar ka bari wasu su yaudare ka, har su kai ka can su baro, saboda shi icce ba a hawan shi ta sama ta kasa ake fra hawan shi, don haka ga fili .nan ka ga mai doki ba a hana ka hawan Kuka ba amma ya dace ka cire takalma kafin kayi hakanwato  ka hau ta saboda ka san tana da santsi sosai bama kamar idan ka taki sa’a an yi ruwa, kana iya fadi watakila ma idan ba ayi sa’a ba ana iya haduwa da karayar da za a dade ana yin jiyya. Masu iya magana sun ce yaro tsaya matsayinka kada zancen ‘yan duniya ya rude ka, haka ma ba neman aure keda wuya ba shige da fici, ita ke bada wahala. Ka tuna fa ba kai daya bane zai yi sha’awar tsayawa neman a zabe shi ba kuna da yawa,  kowa kuma akwai kiwon da ya amshe shi wai makwabcin mai akuya ya sayi kura, ka tuna fa ko a cikin gidan ku ne ake zabe ba dole bane kowa ya zabe  ka ba, bare ma ace har abin ya kai na mazabar kansila bare ma  har ace abin yana kara sama sama ba. Don haka da muguwar rawa gwamma kin tashi, kafin ka yanke shawarar tsayawa takara ko kafin ku yanke tsayawa ayi tunani, wanda zai hana yin a gaba ayi dana sani wanda keya ce saboda kowa ya san a baya take. Ku manta da maganar da ake cewa kowa ya tuka tuwo a tulu, shi ya san yadda zai kwashe, wannan ada ne hakan take faruwa yanzu kuwa duka ne ya yi yawa.

Shugabannin jam’iyyun siyasa tsakaninsu da delegate wato wakilai wadanda sune suke zabe, idan ba akai zuciya nesa ba  ana iya samun matsala idan al’amarin zaben ‘yan takara ya taso kamar dai yadda wannan zabubbukan na ‘yan takarar ake gaba da fara su. Akwai bukatar su shugabannin  siyasa na ko wanne bangare ne, ya dace ace maganarsu ta zama daya su da wakilai masu zabe, saboda a kauce ma sake aukuwar abubuwan da suka faru. Musamman muna iya tunawa da yadda aka yi ta samun rigingimu har a kai ga samun ‘yan takara biyu ga wadanda jama’ a suke so, ga kuma wadanda shugabannin siyasa suke so. Irin wannan matsalar ta taso a jam’iyyar CPC , bayan zabubbukan shekarar 2011 an samu irin wadannan matsalolin, kafin da kuma bayan zabubbukan a Kano akwai maganar Lawal Jafaru Isa da kuma Muhammmed Abacha. A  Jihar Katsina kuma an sha kai ruwa rana dangane wadanda aka tsayar  takarar a kujerun majalisar wakilai ta kasa, haka akan yi ta yin sabarta juyarta.

Da yake yanzu ana gab da shiga yanayin na zaben ‘yan takara saboda zabubbukan shekarar 2019 ‘ masu sha’awar su fafata a zabe su kuma suna ta sayen form na tsayawa a takara. Wannan lokacin ma ai bakon da aka raka yana iya dawowa saboda ai dama watakila ba wani nisa ya yi ba, yanzu jam’iyyar APC kowa ya san da akwai wata wadda ta kunno kai kwanakin baya wadda kiran kan ta da sunan Reform APC, idan ba kashe wutar aka yi ba sosai tana iya sake ruruwa ta kama, kafin kuma a sani an yi wadda ba a son a bata goma biyu bata samu ba. Don haka ba jam’iyyar APC kadai take samun irin matsalar ba, abin yana ma shafa sauran jam’iyyun, tunda ba a rasa son rai da wasu shugabannin jam’iyya za su iya sawa. Ku kuma delegate kun san wanda zai iya kai labari, ko don saboda ya taba  hawa kan kujerar siyasa, manufa anan ya a n zabe shi ya kuma yi ayyukan da suka amfani al’umma, irin wadannan ya dace ku zaba, ba irin masu halayen kaza ba, wadda take samu amma kuma taki dangi. Kada ku kalli amfanin aljifan ku kawai, idan kuka yi haka ana yin zaben tumun dare kenan, duk abin da al’umma suke bukata a ba su shi.

 
Advertisement

labarai