Hamza Dawaki" />

Bukatun Ma’aurata (2)

Kwantar Da Hankali

Matarka tana bukatar samun kwanciyar hankali cikakke daga wurin  ka kafin ka kai ga samun duk wata karfafar gwiwa da abubuwan das u ka kamance ta daga gar eta. Kamar kuma yadda mu ka fara ambatawa a nakon jiya; Kwanciyar hankali bay a nufin jibge mata abinci da kayan matsarofi a gida, ko kuma rundunar masu gadi da kula da lafiyarta. Kwanciyar hankali a cikin zuciya yake. Wato kenan an so ta sami nutsuwa a ranta cewa kai din dai za ka tabbata nata, a yau da gobe. Ba wai a iya yau ba, kuma in rayuwa ta sauya kai ma ka sauya ta. Yawancin mata sukan yi addu’a akasin ta mazajensu a irin wadannan matakai. Wato yayin das hi yake addu’ar Allah Ya kawo budi da watada, ita ko tana can tana addu’ar Allah Ya bar su a wannan mataki har abada. Ba kuma komai ne yake sa wannan ba sai rashin samun kwanciyar hankali.

Samun kwanciyar hankalin dai da muke magana har way au bay a nufin wai kullum dambe ake yi. A’a, ana nufin ta ji kuma ta gamsu har ranta cewa duk ma irin sauyin da ka samu a rayuwa za ku kasance tare. Ba za ga kore ta ka sauya da wadda ta fi daidai da mutum mai cin duniya da tsinke irinka ba. Ba kuma za ka ajiye ta a a gefe kamar wata ratayayyiyar rigar ruwa ba, wadda sai damina-damina in ruwa ya tsananta za a tuno da ita.

Sau da yawa abubuwan da muke furtawa a gaban iyali su ne suke tasiri a zuciyarsu wurin kallon da suke yi mana. Akwai kalamai da dama da za ka furta matarka ta fahimci ai kana tare da ita duk canjinn da za ka samu a rayuwa. Domin za ta ji duk tsare tsaren sabuwar rayuwar da ita ake yin su. sannan akwai wadanda za ka rika yi ta fahimci lallai bad a ita za ka yi sabuwar rayuwarka ba. bayan kalamai ma akwai ayyuka ko motsi ko alamu da mata suke lissafin yaya rayuwarka za ta kasance game da zamantakewa da su. to duk matar da ta fahimci tare kake son yin rayuwa da ita ko da an samu sauyi, to it ace take samun kwanciyar hankali, kuma  ita ce take iya sakin jiki ta karfafa maka gwiwa. Amma kuma duk matar da ta fahimci bad a ita kake shirin sabuwar rayuwarka ba, bat a da wata kwanciyar hankali, kuma ba za ta iya sakin jiki da karfafa maka kwiwa ba. Kuma lallai da maza da dama sun san muhimmancin karfafa gwiwa daga iyalansu da sun saya ko dad a kudi ne!

 

Girmamawa

Daga cikin abubuwan da da yawa daga maza ba sa lura das u akwai girmamawa. Girmamawa tana da muhimmanci kwarai musammam a lokutan dab a ma tsammanin ko jin muhallanta ne. akwai wuraren da muke girmama mata, wadanda dama yawanci su ma sun sa ran za mu girmama su a wurin. Sannan kuma akwai wuraren dab a su zata za mu girmama sun ba, kuma mu ma sai mu ki girmama sun. Amma da za mu girmama su a wannan muhallin, to da sun fi ganin girmanmu mu ma, sannan kuma da girmamawar ta fi burge su. daya daga cikin irin wadannan muhallan, su ne muhallin da za ka yi wa mace kyauta. Mata suna matukar girmama kyauta amma duk   girmama kyautar da mata suke yi, suna da wani abu ɗaya: Duk lokacin da ka ba wa mace kyauta a wulakance, to komai girman kyautar ita kuma ba za ta ga darajar ta ba, ba kuma za ta yi ma godiyar da ta kamata ba! Sau da yawa idan akai aure tsakanin mijin da gidansu ya fi na su matar arziki, ko kuma dai mijin da yake samun kudi kuma yake da damar sayo mata kaya ko ƙayata mata wurin zama da sauran kayan more rayuwa fiye da na baya da ake yi mata a gida. Akan samu kuskure, idan ko da wasa wataran mijin ya sayo mata wani abu, sannan cikin maganganunsa a lokacin da zai ba ta ya nuna mata cewa: A da fa ƙananan kayayyaki kike sa wa wadanda ba su kai wadannan  daraja ba, amma yanzu ga shi nan na zo ina sayo miki manya-manya. Ko dai wata magana makamanciyar wannan da za ta nuna an ƙasƙantar da ita. To haƙiƙa ba za ta taɓa ganin daraja ko son kayan ba. Kuma ba za ta taba yi ma godiyar da ta dace ba. Wataƙila ma ka fita ka dawo ka tarar ba ta dauke su daga inda ka bar su ba.

Don haka dole ne maza su kiyayi yin wata magana ko ishara da tai kama da gori yayin ba wa mata kyauta. Su kuwa mata dole ne su kula da yawaita godiya yayin karbar kyauta. Domin ita ce ke karawa namiji karfin gwiwar ci gaba da yi.

Haka kuma ke ma yayin da yi miki wata kyauta kika ki yin godiyar da ta kamata ko ma kika nuna abin bai burge ki ba, to kamar kina ce mar kar ya kara yi miki kyauta ne. Misali, idan mijinki ya sayo miki wani abu, amma da kika kalli abin sai kika ga ai ba irin wanda ya kwanta miki a rai ba ne. to fa ba nuna mar hakan za ki yi ba. Kamata ya yi ki karba cikin doki, ki yi ta yabon abin kina yi mar godiya. Wannan shi ne zai ba shi karfin gwiwar kara sayen duk wani abu da ya gani, idan ya yi tunanin zai burge ki. Amma muddin kika gwasale abin da ya sayo, to kin kashe mar jiki, kuma farfado da shi ba karamin aiki ba ne, idan ma zai farfado din.

Watarana  aljihuna ya yi sakayau. Sai na tafi kamfanin yayana na man gyada, na je na kusa yini ina ta aiki. Mun fito muna hutawa, sai na ga wani mutum yana tallan wasu kananan turame masu kyau. Nai kiransa mu kai ciniki, na sayi daya, tun kafin a biya ni. na ce wa yayana

“Ba ni dari biyar na sayi turmi.”

Sai ya kalle ni cikin mamaki, ya ce da ni: “Wace irin hauka ce wannan, ka gama yin aiki amma ka sayi turmi na kusan duk kudin!”  Na yi dariya na ce

“Kawai na san za ta so turmin ne.”

Kafin in zo gida kuma mutane da yawa sun rika yabon turmin da mamakin araharsa. Amma da na zo gida matata ta karba ta ce:

“Kuma nawa?” Cikin kuzari na ce mata

“Dari biyar!”  Sai na ji ta ce:

“Kai amma ya yi tsada wallahi!”

Jikina ya yi matukar sanyi nan take. Kuma tun daga wancan lokacin duk lokacin da zan sa yi wani abu in kai gida sai na tuna wannan ranar. Na sha kin sayen abubuwa da dama kuma saboda wannan tunanin.

Wadannan wasu ne daga cikin bukatun da ma’aurata suke son samu a wurin abokan zamansu. Fatanmu shi ne mu lura b da abuubuwan da abokan zamanmu suke so, mu rika yi musu. Kuma mu kauracewa wadanda suke kashe musu gwiwa.

Exit mobile version