BULALIYA: Siyasar 2019 A Nijeriya: A Yi Haramar Tattara ‘Sididi,’ A Mayarwa Mai ‘Sadada!’

Tare da Al-Amin Ciroma 08033225331 (TES Kawai )   ciroma14@yahoo.com   

A Yi Haramar Tattara Sididi, A Mayarwa Mai Sadada! Siyasa rigar ‘yanci kowa da irin tasa! Taken da ake yi wa siyasa kenan a kasashen Afrika kamar Nijeriya. Irin haka tasa a duk lokacin da aka fara motsa jiki game da zabuka hankula kan tafi ne ga irin wadanda za su fito takara.

Bisa hakan ne nake son yin sharhi kan halin da ‘yan siyasa suka jefa talakawa sannan suka yi watsi da dukkanin alkawuran da suka yi a baya. Ba kuma za mu cimma hakan ba, sai mun yi waiwaye kan wasu muhimman abubuwan da suka faru a baya.

Bari mu duba zazzafar siyasar da aka tafka a shekarar 2015 tsakanin magoya bayan jam’iyya mai mulkin lokacin – PDP da kuma babbar jam’iyyar adawa a sa’ilin nan – APC. Ana kiris da fara zabukan ne ‘yan siyasan suka soma matsa kaimin ganin sun sami dimbin goyon bayan talakawa da masu kada kuri’a. Babban abin da ya bai wa al’umma takaici da almara shi ne yadda APC da PDP suka rika musayar yawu tare da yakar juna da lafuza marasa tushe gami da alkawuran da su kansu, sun san cewa zance ne kawai ba za su iya cikawa ba!

Kamar yadda na fadi a sama, wannan nazarin zai kasance hannunka mai sanda ne ga ‘yan’uwana ‘yan Nijeriya tare da yi musu manuniya kan yadda ‘yan siyasa ke wofintar da su da zarar sun zabe su, sannan daga baya su kara dawowa cikin wata siga, su kara yaudarar al’umma musamman talakawa.

A shekarar 2015 ne fa wasu daga cikin ‘yan siyasa, wadanda giyar mulki ta rufewa idanu, suka rika yin babatu da shirme iri daban-daban da sunan bajinta a fagen siyasa. Wasu daga ciki na ban dariya ne, misali; Tsohon Ministan Yada Labarai Mista Labaran Maku, ya bayyana duhun jahilcinsa miraran a idanun duniya, inda ya ce, “Muna godiya ga Shugaba Goodluck Jonathan da ya kawo mana shafin ‘Facebook’ a Nijeriya,” kaico!

Wannan ya fi kama da takaici maimakon abin dariya! An wayi gari, saboda rashin tantancewa, ana zaben kowane irin mutum a ba shi babban mukami a fagen siyasa, har aka maka babban kuskure, aka zabi Maku!

Har ga Allah bai ma san halin da duniyar yanar gizo ko intanet take ciki ba, ballantana ya iya bambance shafin sadarwan da Mark Elliot Zuckerberg ya kirkiro, wato ‘Facebook,’ ya koma ya jingina nasarar shafin ga maigidansa! Wannan kenan.

Shi ma kansa tsohon Shugaba Jonathan, ya tafka babbar katobarar, a yayin da ya rage saura ‘yan kwanaki ya bar gadon mulkin kasar nan, inda ya ce, “Kusan kashi 70 a cikin 100 na handama da babakeren da ake tafkawa a Nijeriya ba komai ba ne illa ‘yar karamar sata ce kawai!”

Haka shi ma tsohon Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang, a daidai lokacin da askin ya zo gaban goshi ana shirye-shiryen zabe, ya bude wagegen bakinsa ya ce, “Allah da kan sa ma dan dimokuradiyya ne, bai dai yarda da magudi ba, amma idan ka yi sa’a ka tafka magudin har ka yi nasara, tabbas Allah ya amince da hakan!”

Hatta shi ma kansa Ministan Sufuri na yanzu, Rotimi Ameachi, wato Tsohon Gwamnan Ribas, ya taba yi wa talakawa gatse a daidai lokacin da yake gudanar da yakin neman zabensa, ya ce: “Ba zan mutu ba don ina shan ruwan roba ne! Ku kuma ruwan korama da na fanfo kuke sha!”

Kafin mu hattama wannan nazarin yana da kyau mu kalli halin da wannan kasa tamu take ciki. Rigingimu daban-daban ke dosu mu. Matsalolin yau daban da na gobe. Anya ‘yan’uwana ‘yan Nijeriya suna lissafin dimbin nasarorin da Allah Ya ba wa kasar kuwa? Babbar nasarar da Allah Ya ba Nijeriya shi ne al’ummarta na matukar kaunar zaman lafiya. Dalilina na fadin haka shi ne, kowannenmu ya san irin halin da kasar Rwanda mai kimamin al’umma milyan bakwai ta samu kanta ciki, sanadiyyar wata ‘yar hatsaniya.

Ko an manta rigimar da ta barke a tsakanin ‘yan kabilar Hutu da Tutsi a kasar? Rigimar ce fa ta yi sanadiyyar salwantar rayuka sama da milyan daya a cikin kwanaki 100 kacal!

Idan za a iya tunawa an fara rikicin na kasar Rwanda ne a ranar 7 ga Afrilun 1994, aka kammala a Yulin shekarar, amma komai sai da ya tsaya cak a kasar. Babbar tambaya a nan ita ce, masu muradin kawo rudani a Nijeriya, yaya suke ganin makomarta idan ba a kai hankali nesa ba?

Yanzu dai bari mu ari hikimar masu zance da ke cewa ‘Ruwa a cikin cokali ya ishi mai hankali yin wanka!’ Duk mai hangen nesa tare da kyakkyawan nazari ya san cewa akwai ‘yan siyasan Nijeriya suna da manyan matsaloli, wadanda ke bukatar karatun ta-natsu wajen warware su. Zai fi kyau mu kalli yadda salon siyasar ya dauki sabon alkibla don mu fuskanci manyan kalubalen da ke gabanmu a shekarar 2019 idan Allah Ya nufe mu da kai wa.

Ko ba komai dai, ya kamata a kasa sanin cewa  Nijeriya fa kasa ce wacce Allah kadai ne ke sonta! Dalilin da ya sa har Ya azurtata da dimbin albarkatu mara iyaka. Mu koma mu kalli ragamar shugabancin kasar a matakai daban-daban da wadanda ke rike da ita, kamar haka:

*A cikin ‘yan majalisun jihohin nan kusan 900 da Musulmi ciki, akwai Kirista.

*Daga cikin shugabannin kananan hukumomin nan 774 na kasar akwai Musulmi har ila yau akwai Kirista.

*Ministoci, Kwamishinoni, Kansiloli da masu taimaka wa gwamna a fannoni daban-daban ma akwai Musulmi akwai Kirista.

Babban abin lura a cikin wannan jerin da na kawo kamar yadda kowa ya sani shi ne, Musulmi wadanda Allah Ya ba su dama su kan tafi Hajji da Umrah, bayan haka su kan yi Sallah sau biyar a yini guda, ga Sallar Jumma’a ga Azumi da sauran ibadojin da addinin Musulunci ya kwadaitar. A daya gefen kuma Kiristoci kan tafi aikin Hajji a kasar Isra’ila, su kan gudanar da ibadojinsu daidai da koyarwar addinin Kirista.

Duk da irin wadannan matakan da shugabanninmu ke kai, sai dai Babban Bankin duniya ya bankado da wata badakalar Dalar Amurka Bilyan 600 da aka sace a farfajiyar shugabancin Nijeriya! Wadanda aka san suke tafka wannan ta’asa su kan tafi Masallatai ko Majami’ai don gudanar da addininsu! Babbar tambaya a nan ita ce, me suke koyowa a wuraren ibadun nasu?

Alal-misali, me ya sa Musulmi ba zai rika tunawa da rantsuwar da yake yi da Alkur’ani a ranar da yake kama aiki ba? Don me kake tunanin harkar siyasa ba ta shafi addini ba? Ko kana tsammanin idan ka karkatar da dukiyar al’ummar, Allah ba zai kama ka da hakki ba?

Ko ma dai me? Kamar yadda na yo shimfida a farkon wannan ‘Bulaliyar,’ shekarar 2019 na nan tafe, kiran da zan yi wa al’ummar Nijeriya da babbar murya shi ne kada su bari a yaudare su da addini don neman kuri’a.

A natsu a san wadanda za a dora a fagen shugabanni nan gaba. Don haka na ari kalmomin Mawaki Mudassir Kasim, nake cewa a kwana da shirin bincikar halayen mutum tsaf kafin a zabe shi ko da Kansila ne. Idan yana da halayen kwarai kuma adali ne, sai a zabe shi. Idan kuma ba haka ba ne, a mayar da kayansa! Don haka a yi haramar tattara Sididi, a mayar wa mai Sadada!

 

 

Exit mobile version