Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta bai wa majalisaun kananan hukumomin APC cikakken goyon baya domin su tsaya da kafafunsu wajen gudanar da ayyukan ci gaban al’ummar yankunan su, bayan kammala zaben kananan hukumomin mai zuwa a ranar 27 ga watan Fabarairun 2021 a Yobe.
Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana hakan a lokacin da ya mika tutar jam’iyyar APC ga yan takarar shugabancin kananan hukumomin jihar 17 a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Damaturu ranar Jummu’a.
“Saboda mu na son kawo karshen yanayin da idan ka je kananan hukumomi ka samesu a bushe. Kuma za mu damka shugabancin su a hannun mutanen da suka dace, wanda kuma a duk lokacin da aka sake wa kananan hukumomi mara, ya kasance su na aiki cikin yanci da walwala, hakan zai taimaka wajen rage wa gwamnatin jiha matsaloli da wahalhu.” In ji Buni.
Har wala yau kuma ya ce gwamnatin Yobe za ta bai wa kananan hukumomin cikakkiyar dama wanda zai basu zarafin gudanar da mulkin rukunin gwamnati na uku (karamar hukuma) cikin tsanaki.