Muhammad Maitela" />

Buni Ya Ziyarci Aikin Ginin Kasuwannin Zamani A Gashuwa Da Nguru

Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya ziyarci aikin ginin kasuwanin zamani da hanyoyin mota na biliyoyin Naira, wanda gwamnatin jihar ke aiwatarwa a Gashuwa da Nguru a jihar a karshen mako.

Tawagar Gwamna Buni wadda ta manyan kusoshin gwamnatinsa mataimakin gwamna da Kakakin majalisar dokokin jihar, a lokacin ziyarar, ya nuna gamsuwa da ingancin aikin tare da yadda ayyukan ke gudana bisa yadda aka tsara da yan kwangilar.

Gwamna Buni ya bayyana cewa, “ko shakka babu wadannan ayyukan za su bunkasa rayuwar al’ummar wadannan kananan hukumomi da jihar Yobe baki daya, haka kuma mun yaba da ingancin aikin.

“Bugu da kari kuma, za mu yi alfahari da wadannan ayyukan saboda tasirin da za su yi ga cigaban jama’a da zaran an kammala su, ayyuka ne wadanda za su taimaka wajen bunkasa ci gaban tattalin arzikin jama’ar wannan yanki da jihar Yobe bakidaya.”

A hannu guda kuma, Gwamnan ya bai wa yan kwangilar tabbacin cewa a kowane lokaci gwamnatin jihar a shirye take wajen biyan su kudaden su a duk lokacin da su ka kammala ayyukan.

Har wa yau, Gwamna Buni ya zagaya wuraren da ake ginin kasuwanin zamanin tare da hanyoyin mota a garuruwan, wanda ya bayyana gamsuwar sa dangane da yadda ayyukan ke gudana. Wanda kuma ya bukaci yan kwangilar su kammala ayyukan cikin lokacin da aka kulla yarjejeniya.

Exit mobile version