Ministar jinkai, Hajiya Sadiya Umar Farouk ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gina gidaje da sauran ababan more rayuwa a cikin kasar nan kamar irin su tashoshin jiragen sama da tashoshin jiragen kasa da tashoshin mota da makarantu, domin taimaka wa nakasassun mutana a Nijeriya. Wannan yana cikin bayanin da mashawarcin ministar a kan yada labarai, Nneka Ikem Anibeze ya rattaba hannu. Ministar ta yi wannan roko ne lokacin da take gabatar da jawabi a gaban shugaba da sakataren hukumar kula da nakasassun mutane a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Sadiya ta bayyana harincikinta ga shugaban kasa bisa irin tarban da ya yi wa hukumar kula da nakassu ta kasa, inda ta bayyana cewa, lallai an yi watsi da samar da ababan more rayuwa a yankunan nakasassu da ke fadin kasar nan. ta kasa da cewa, sama da kashi 95 na gine-ginen gwamnati da ke cikin kasar nan ba a bai wa nakasassun mutane ba, kuma suna bukatar su da samar musu da na’urori da zai taimaka musu wajen bunkasa iliminsu. Ministar ta ci gaba da cewa, ma’aikatarta a karkashin shirin bunkasa jari za ta samar wa nakasassun kayayyaki ga yankunansu.
“Akwai bukatar daukan matakan da suka dace wajen tallafa wa rayuwar nakasassun mutane ta hanyar fadakarwa da zai rage nuna musa bambamci da taimawa rayuwarsu. Akwai bukatar samun bayanan nakasassu a cikin kasar nan domin ba su takardar shaida wanda za a tabbatar da taimaka musu ta karkashin gwamnati.
“Mun sami nasarar ceto rayuwar dubban nakasassu ta hanyar mabambamtan shirye-shiryanmu wanda muke gudanarwa a cikin kasar nan,” in ji ministar jinkai
Da yake mayar da jawabi, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bukaci hukumar kula da nakasassu ta kasa ta yi kokarin taka mahimmiyar rawa a karkashin shirin gwamnati na ceto mutane miliyan 100 daga kangin talauci a Nijeriya. Shugaban ya ci gaba da bayyana cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da kokari wajen inganta rayuwar nakasassu a Nijeriya.
“Ba kuskure ba ne da aka ba ku mukami wajen kulawa da nakasassun mutane da suke cikin al’umma a Nijeriya, domin kun yi kokari wajen bin dokokin wannan hukuma da gwamnatin tarayya ta samar domin ceto rayuwar nakasassu a Nijeriya.
“Aikin wannan hukuma yana da matukar yawa. Yana daya daga cikin ayyukanku wajen tabbatar da ganin gwamnatin tarayya ta baba rayuwar gaba daya ‘yan kasa musamman ma nakasassu da ke Nijeriya.
“Nijeriya ta rattaba hannu da Majalisar Dinkin Duniya wajen inganta rayuwan nakasassu wajen inganta rayuwarsu da kuma abubuwan da suke bukata a duniya. A karkashin gwamnatina, zan ci gaba da kokari ta kowani fuska wajen bunkasa rayuwar ‘yan kasar nan da kuma dakile matsaloli da suke fuskanta a duk wani lungu da sako da ke fadin kasar nan,” in ji shi.
Tun da farko dai, majalisa ta amince da bai wa Hon. Dakta Husseinin Hassan Kangiwa , dan asalin yankin Arewa maso Yamma a matsayin shugaban hukumar kulada nakasassu ta kasa, kanar yadda sashi na 32 (3) da 40 (1) ya tanada karkashin dokar da ya samar ta hukumar a shekarar 2019.
Sauran mambobin hukumar sun hada da Misis Esther Andrew Anwu da Mista Abba Audu da Misis Amina Rahma Audu da Mista Jaja Oparaku da Misis Philomena I Konwea da Mista Omopariola Busuyi da kuma Mr. James Dabid Lalu a matsayin sakataren hukumar.