Bunkasa Rayuwar Al’umma Shi Ne Babbar Buri Na —Hajiya Lami Kyari

Hon. Hajiya Lami Kyari Joda (Alkaman Gudi) na daga cikin ‘yan takara na gaba gaba a neman shugabancin karamar hukumar Fika ta jihar Yobe a karkashin jam’iyyar APC, ta bayyana cewa, kaunar cigaban al’umma ne abin da ke a gaban ta a fafutukar takarar da ta ke yi na shugabancin karamar hukumar Fika, ta bayyana haka ne a tattauanwar ta mamena labarai kwanakin baya.

Hon. Hajiya Lami Kyari waddda ake sa ran za ta kafa tarihin zama mace ta farko da za ta mulki karamar hukumar Fika ta ce, ‘Da farko kafin in fara kira gare su, shi kansa takaran al’umma ne suka bijiro shi da kansu, yaran su suka fara tallata ni a social media, ni sai dai kawai gani nake abubuwa suna wucewa, manya suka shigo ciki suka ce ki cigaba abin na Allah ne kuma zai shige mana a gaba” inji ta.

Al’umma sun cigaba da bayyana cewa, “Muna lokaci ya yi da za a saka maki saboda kin dade kina bauta a wannan jam’yyar, saboda haka sako da fatan alkairi da Adduoi da ‘yan karkara suke min. akan haka za ka fahinci cewa, wannan takara ta abu ne na tafiya da al’umma gaba daya.

Daga na ta kuma yaba wa Gwamnan jihar Yob Mai Mala Buni akan yadda yak e gudanar da ayyikan ciga a sassan jihar, t ace, jihar Yobe ta fada hannun jagoranci na gari, akan haka ta bukaci al’umma jihar s cigaba da bayar da goyon baya ga ayyukan cigab da Gwmann ya ke yi.

Exit mobile version