Bunkasa Rayuwar Al’umma Shi Ne Babbar Buri Na – Hon. Hajiya Kyari Joda

Hajiya Kyari Joda

Daga Bello Hamza, Abuja

A wannan filin namu da ke zakulo muku fittatun mata da suka yi fice a harkokin da suka sa a gaba  a fadin tarayyar kasar nan, a yau zamu kawo muku tarihi da tsarin siyasar wata kallabi a tsakanin rawunna, wato Hon. Hajiya Kyari Joda (Alkaman Gudi), mace ta farko da ta dare karagar shugabancin karamar hukuma a fadin jihar Yobe, wato Shugabar karamar Fika da ke yakin Arewa maso Gabashin Nijeriya, wanda aka kuma yi mata shaidar gudunar da mulki tare da tausayin al’umma, don kuwa daga hawanta karagar shugabancin karamar hukumar Fika ta gudanar da ayyukan da akayi fiye da shekara 20 ba a yi ba a wasu wurare na karamar hukumar.

Hon. Hajiya Halima Kyari Joda ta lashe zabe ne a karkashin jam’iyyar APC a zaben  da aka gudanar ranar 27 ga watan Fabrairu 2021 ta kuma shiga ofis don fara aiki a ranar 14 ga watan Maris 201, inda bata yi wata-wata ba ta fara aiwatar da alkawurran da ta yi wa al’umma a lokacin yakin neman zabe, musamman ganin tun da farko ta riga ta yi nazarin irin matsalolin da ke fuskantar al’umma karamar hukumar wadanda suka hada da bukatar samar da ruwan sha, kiwon lafiya, matsalar tsaro, samar da ingantattce ilimi da kuma bunkasa harkokin kasuwanci, musamman ganin yawacin al’ummar karamar hukumar Fika noma ne da kuma kasuwanci ne babbar sana’ar su.

Daga hawanta ta tunkari yadda ta za ta yi maganin matsalar ruwa da ake fuskanta a yankin karamar hukumar Fika, ta kuma fara ne da zagaya yankin karamar hukumar don ganin yadda lamarin yake, da farko ta ziyarci garin Janga Malam Garba, inda lamarin ya fi kamari, inda ta samu rakiyar mataimakinta da kuma babban sakataren karamar hukuma, zaiyarar ta ya matukar sosa wa al’umma yankin rai don kuwa wannan ziyzra nata shi ne na biyu daga wani shugaban karamar hukumar Fika a fiye da shekara 20 da suka wuce, sana’a da harkokiun al’umma yanin shi ne noma da kiwo suna kuma fuskantar matsalar samun ruwa don gudamar da harkokinsu, don sai sun yi kusan tafiyar fiye dana mituna 34 kafin su samu ruwan sha mai tsafta. Bayan wannan ziyara ne, Hon. Halima Kyari ta garzaya ofishin hukuma ruwa ta jihar in a ta nemi taimakon su na gaggawa, kuma duk da haka a ranar 10 ga watan Afrilu 2021 tare da rakiyar ‘yan majalisarta da ma’aikatar hukumar ruwa na jihar suka dira garin nan Janga Dagauda inda suka gudanar da aikin farfado da dukkan rijiyoyin burtsatsae da suka lalace wanda sun kai 13, sun kuma hada da na yankin Jangadagauda, Nahuta Godowoli, Zayi, Bulakos, Janda, Jurmi nazari, Turmi Karekare, Tumbulwa, janje, Jange bulan, Garin Zomo, Bakuna, Lewe, Garin Bura. Wannan gaggarumin aaikin ya dadada wa al’umma rai don kuwa masu iya magana na cewa, RUWA ABOKIN AIKI.

Wani babbar matsala da kuma ke addabar al’umma yankin Arewa maso Gasa gaba daya shi ne al’amarin tsaro, karamar huumar Fika ita ma ta fuskanci matsala da harkokin ‘yan ta’adda da yankin ke fuskanta, a kan haka Hon Halima Kyari ta tallafawa jami’an tsaron karamar hukumar da kayan aiki inda ta samarwa da rundunar ‘yan sanda da kuma kungiyar ‘yan sintiri na karamar hukumar da mota kirar Hilud don su ji dadin gudanar da ayyukan sintiri a fadin karamar hukumar. Hon. Halima Kyari Joda ta kuma jagoranci sasantawa don tabbatar da zaman lafiya a tsaanin manoma da makiyaya a fadin karamar hukuma, haka kuma tana shiga don ganin ana samun zaman lafiya a tsakanin al’umma gaba daya, hakan ya sa masu lura da al’umurran yau da kullum suka fahinci cewa yanzu an samu raguwa zirga zirgar al’umma a kotuan yankin don tun a gida ake yin sulhu, hakan kuma ya wanzar da fahinytar juna a tsakanin al’umma.

A bangaren samar da ingantatacen kiwon lafiya ga al’umma karamar hukumar Fika kuwa,Hon Halima Kyari ta fara ne da kai ziyara yankin karamar hulumar don ganin irin halin da cibiyouin kiwo lafiya suke ciki, ziyara ya kuma nuna mata irin halin gurbacewa da asibitocin yankun suke ci, inda ta gabatar wad a kwamishin lafiya cikakkne rahoton halin da cibiyn kiwon lafiyar suke ciki, ta kuma kai wanna ziyara ne tare da rakiyar masu ruwa da tsaki a karamar hukumar. Tabbas wanan hobbasa ya taimaka wajen zabura da gwamnatin jihar wajen kawo bangaren dauki, a halih yanzu al’umma a karamar hukumar suna ta godiya das a albarka a kan wanna kokaron na Hon Halima Kyari.

Kasancewar ilimi shi e ginshikin rayuwar al’uMma, haka kuma ya sanya gwamnan jihar ya kaddamar da dokar ta baci a bangaren ilimi saboda bukatar fafado da yankin, hakan ya sa Hon Halima ta rungumi wanan tsari na Gob Mai Mala Buni. Bayan taro na tattauanawa da masu ruwa da tsraki a bangaren ilimi na karamar hukumar tare da kuma ziyara ga wasu makarantu a karamar hukumar don ganin halin da suke ciki. Ta kuma nemi tallafi daga kungiyoyi masu zaman kansu na cikin da kasashe waje, kamar s UNDP, SEMA , da ma’akatar ilimi na jinar Yobe. Hakan kuma yana haifar da da mai ido, don kuwa a halihn yanzu al’amurra sun yi matukar canzawa a bangaren ilimi.

Kasancewar yawancin al’ummar yankin karamar hukumar Fika Nima da kasuwanci ne babar sana’arsu, daga hawanta karahar shugabancin karamar hukumar Fika, Hon Halima Kyari ta zauna tare da yin nazari mai tsawo na neman hanyoyin da za ta samar da mafita a bunkasa harkar noma da kasuwanci a karanmar hukumar, wanda haka ya kai ga shirin gina kasuwar Ngalda tare da wani shiri na musamman da kungiyar UNDP don gina bangaren sayar da shanu da hatsi da sauran kayan masarufi, wanna kuma za kara bunkasa harkokin rayuwar al’umma, za a kuma rage zaman kashe wando a tsakanin matasa a karamar hukumar. Domin bunkasa rayuwar matasa Hon. Halima Kyari ta yi hobbasa ta hanyar samar wa matasa gurbin karatu a ‘College of Admin and Management Studies da ke Damaturu’ ta kuma fara nemar wa ‘yan asalin karamar hukumar gurbi a makarantar School of Nursing Damaturu, haka kuma ta jagoranci samar da tallafi na koyon sana’o’in dogaro da kai ga matasa maza da mata a karamaru hukuma, inda aka koya musu sana’o’I daban daban tare da kuma basu kayan aiki, kamar su injin nika da kekuna dinki da sauransu.

Ga wanda ya dade bai ziyarci hedikwatar karamar hukumar ba zai kasa gane wasu wuarre don kuwa Hon Halima Kyari ta jagoranci sabunta kayan aiki na ofis ofis ta hanyar samar da sabbin kujeru da talabijin da AC, wanda hakan ya kara wa ma’aikata hazakar gudaar da ayyunkan su. Haka kuma ma’aikata a karamar hukumar na mika godiya saboda zuwa yanzu tunda Hon Halima Kyari ta dare kara albashi da alawus alawus na ma’aikatan karamar hukumar sun nuna jindadin su akan yadda Hon. Halima Kyari Joda  ke kula da ganin ana biyansu hakkokinsu akan lokaci ba tare da bata lokaci ba.

 

Exit mobile version