Connect with us

RAHOTANNI

Bunkasar Hukumar Shige Da Fice A Karkashin CGI Babandede

Published

on

Hukumar Shige da fice ta Nijeriya (NIS) a karkashin jagorancin shugabanta mai sanin makamar aiki, mai dimbin hangen nesa Muhammad Babandede MFR, wanda ke hankoron kawo sauyi don ci gabantar da ayyukan hukumar ta shige da fice, wannan hankoron ya dakile babakere sannan ya samar da tsimi da tanadi, ya haifar aikin hukumar mai nagarta, dadin-dadawa ofisoshin hukumar da ke a fadin kasar nan ma ba a barsu a baya ba wajen samar da kudaden shiga.

Wannan ya zama kamar al’adar hukumar ne, duk shekara tana fara wa ne da sabbin shirye-shirye, sabbin ayyuka da abubuwan da take son cimma, wannan shekarar ta fara ne da gabatar da sabon fasfo, wacce hukumar ta gabatar ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 15 ga watan Junairu, inda hukumar ta mika wa shugaban kasar fasfo dinshi mai tsawon wa’adin shekaru 10, haka shima mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya samu nashi fasfon, wannan shine sumin tabi na fara bada wannan fasfo wanda hukumar karkashin jagorancin Babanded ta fara. Wannan ba karamar nasara bace ga hukumar, saboda takardar fasfon tana da matukar muhimmanci a fadin duniya gaba daya, sannan gashi tana daga cikin abubuwan da suke samar wa kasa da kudaden shiga, karin karfin gwiwa ne da gogewa ga jami’an hukumar a duk fadin kasar nan.

Dole a ambaci shirye-shiryen hukumar na tsare-tsare da dabarun kula da kan iyakokin kasa na shekarun 2019-2023, wannan shirin ya samu sharhi da fashin baki daga masana da kwararru a fannin kula da iyakokin kasashe, inda suka tabbatar da cewa shirin ya dace da tsarin kula da kan iyakoki na zamani, kuma zai yi matukar tasiri a gudanar da ayyukan hukumar, ciki kuwa harda tsaron kasa. A cewar masanan wannan shirin zai taimaka wajen tsare iyakokin kasa, sannan zai dakile ayyukan rashin gaskiya da baragurbi suke aikata musamman a kan iyakoki, in kuwa aka samu damar dakile miyagun laifukkan, hakan na nufin za a samu habbakar tattalin arziki. Shirin na tsare-tsare da dabarun kula da kan iyakokin kasa (na shekarun 2019-2023) wanda hukumar karkashin jagorancin Babandede ta gabatar namijin kokari ne, wanda zai kasance ya bunkasa ayyukan jami’an hukumar a kan iyakokin kasa gaba daya, sannan zai dace da fasawar kula da kan iyakoki na zamani, kamar yadda yake a kasashen duniya da suka ci gaba.

Samun nasarar wannan tsarin na tsare-tsare da dabarun kula da kan iyakokin kasa ya tabbata ne da samar da tsarin kula da bayanai na kan iyakokin kasa (Border Management Information System) ta hanyar amfani da wani tsari na daban, wato (Migration Information Data Analysis System) wato tsarin taskace bayanan shige-da-fice, duk dai hukumar a karkashin jagorancin Babandede ta samar da wannan, inda aka shigar da tsarin zuwa manyan filayen jirgin sama, kan iyakokin kasar nan, da ma tashoshin jirgin ruwa, duk don samar da tsarin mai sauki na karbar bayanan matafiya, da kuma samar da takardun tafiya da bayanan matafiya. Wannan tsarin ya tabbatar da an fadada aikin tattara muhimman bayanan masu shige da fice, musamman a gurare daban-daban har 15, wanda kusan shine adadin shingen kan iyakokin kasar nan.

A matsayin matakin farko na kula da iyakar kasa, shirin MIDAS zai samar da fasahar da zata hade dukkan iyakokin kasar nan, da ma bayanan dukkan matafiya, don ganin Nijeriya ta cimma ka’idar da hukumar ICAO da kuma kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya suka bayar mail amba 2396.

Wani muhimman abu da ba a cika damuwa da shi ba daga cikin ayyukan da hukumar karkashin jagorancin Babandede ta gabatar, akwai yaki da fasa kwaurin mutane, da kuma dakile safarar mutane.

Hukumar karkashin Babandede ta samar da tsarin kula da iyakokin kasa, wanda yake aikin taskace matafiya ta hanyar amfani da fasahar zamani, shirin ya samu nasarar faraway tare da halartar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar 12 ga watan Yulin Shekarar 2019. Shirin ya sake samar da hanyoyin kara tsuke kan iyakokin kasar, ta hanyar tabbatar da duk wadanda suka shigo kasar sun shiga rijistar musamman baki da ba zasu wuce kwanaki 90 ba, a lokacin da wata shida na afuwa da Shugaban Kasa ya bayar suka wuce a watan Junairun shekarar 2020.

Tunda aka fara wannan tsarin zuwa yanzu an yiwa bakin haure akalla 255,000 rijista a cibiyoyin rijistar zamani da suke a afdin kasar nan, wannan ya kara dankon alakar aiki tsakanin hukumar shige da fice (NIS) da hukuma mai yaki da safarar mutane (NAPTIP), sannan ya karfafawa al’ummar Nijeriya gwiwa a aikin hukumar na dakile annobar safarar mutane da ta zama ruwan dare, hakazalika hukumomin kasa da kasa su ma sun samu wannan karfin gwiwar. Samarda bayanan bakin haure, ba karamar nasara ba ce da duk wanda yake bibbiyar lamari zai yarda cewa hukumar ta kama hanyar cimma manyan nasarorin da za su taimaketa wajen zama daya daga cikin hukumomin shige da fice masu sannin makamar aiki da dacewa da zamani, hukumar ta na tattara wadannan bayanan ne ta filayen jirgin sama, takardun izini shigowa kasa, takardun fasfo, kan iyakokin kasa da na ruwa, takardun izinin zama da sauran hanyoyi da hukumar ta tanada.

Aikin bada fasfo yana daga cikin muhimman ayyukan da hukumar karkashin shugabancin Babandede ta saka a gaba, musamman inganta wannan bangaren. Jim kadan da fara gabatar da sabon takardar fasfo wanda Shugaban Kasa Buhari ya jagoranta, hukumar ta ci gaba da aikin bada takardun fasfo a ilahirin jihohin Nijeriya a cikin watan Mayun shekarar 2019, hukumar ta bada fasfo sama da miliyan biyu, hukumar ta samar da tsarin bibbiya da kai, ga cibiyoyin samar da fasfo din na gaggawa, sannan fasfo din ya dace da tanajin dokokin hukumar ICAO ta kasa da kasa, wannan sabon fasfon din kamar mafarki ne ya zamo gaskiya ga al’ummar Nijeriya, musamman ma dai wadanda suke rayuwa a kasashen ketare, an fara aikin bada wannan fasfo dinne a ofisoshin hukumar dake jihohin Abuja, Legas, Kano da Fatakwal, sannan zuwa yanzu ana shirye-shirye fara aikin bada wannan fasfon din a kasashen waje, inda za a farad aga ofishin jakadancin Nijeriya dake birnin Landan.

Fasfon din Nijeriya, yana daga cikin muhimman takardun da ya samu ci gaba a tsakanini shekaru uku, a kan wannan aikin na samar da ingantaccen fasfo, hukumar ta samar da muhallin aiki ga jami’ai na musamman masu ayyukan kula da kan iyakokin kasa,  an samar da muhallin ne a tsakiyar birnin tarayya Abuja, musamman ga mataimakan kwanturola na hukumar, sai kuma wasu muhallan da zasu zama cibiyoyin aiki ga manyan jami’ai na yankunan kasa, sai ofisoshi na wasu manyan jami’ai a fadin Nijeriya, dadin dadawa sai muhallin zama ga kananan ma’aikata a duk fadin kasa, wanda zai dace da barikin zaman jami’ai. Hukumar ta samar da tasoshin shan mai na jami’an hukumar, tashar kashe gobara, kantunan cefane wanda kungiyar matan jami’an hukumar suka samar, da ma sauran ayyukan da hukumar ta samar don inganta ayyukanta da ba zasu lissafu ba a fadin kasar nan.

Hukumar Shige Ficen (NIS) ta kaddamar da tsarin takardar shaidan shekarar 2020, wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a watan Fabrairun shekarar nan da muke ciki, hukumar ta na ta gudanar da shirye-shirye da ayyuka ba kama hannun yaro, inda ta yi fintinkau musamman a yankin yammacin Afirka, inda har shugabannin hukumomin shige da fice na sauran kasashen yankin suka ziyarci shugaban hukumar na Nijeriya, Muhammad Babandede don tattaunawa makamar aiki. Babanded wanda zakakuri ne a fagen aiki, ya yi amfani da kwarewarshi ne wajen tabbatar da hukumar ta samu wannan nasarar, jami’in bai tsaya a kan aiki ba kadai, ya tabbatar da ya gyara dabi’un jami’an hukumar, ciki kuwa harda tsarin sanya kayan aiki, samar da ilimin zamani ga dukkan jami’ai. Wannan namijin kokarin da babban jami’in ya yi sun samarwa da Nijeriya damar gudanar da harkokin tattalin arziki masu karko, musamman fannin yawon shakatawa, wanda yanzu ake samun takardun izini a saukake ta shafukan yanar gizo, sannan a biya kudi ma a take ba tare da wata matsala, wannan tsarin kuma ya yi maganin bata gari masu amfani da wannan damar don zambatar al’ummar, hukumar mai ma’aikata mutum 26,000 tana da ofisoshi a duk ilahirin jihohin Nijeriya 36, da kuma birnin tarayya Abuja, kananan hukumomi 774 suna da cibiyoyi na hukumar, sannan hukumar tana da wasu cibiyoyin 52a kasashen duniya daban-daban wanda jami’anta suke gudanar da ayyuka. (DCI JAMES SUNDAY PCC, JAMI’IN HULDA DA JAMA’A NA HUKUMAR SHIGE DA FICE TA KASA, HEDIKWATA, ABUJA) imel: immigrationspro@gmail.com
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: