Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano
Idan dai ana batun kasuwanci, musamman a irin wannan lokaci da gwamnatoci ke kokarin ganin an habbaka harkar Noma da Kasuwanci, Kasuwanni irin Kantin Kwari, Kasuwar tufafi mafi girma a Arewacin Sahara na sahun gaba wurin la’akari da makomar kasuwanci musamman a cikin Nijeriya.
Alhaji Muhammad Abdullahi (Dubji) na cikin mutanen da suka ga lokacin da Kasuwar ta Kwari ke hannun bakin haure irin Indiyawa da Kwarori, saboda haka ya fedewa Jaridar Leadership A Yau biri har bindinsa yadda gwagwarmaya ta kasance tun shekara ta 1972, yau shekara 45 Kenan da dawowar wannan kasuwa hannun ‘yan kasa.
Ya ce; “sojoji ne suka samar da dokar mayar da kasuwanci hannun ‘yan kasa a Nijeriya. Ya kara da cewa, wannan doka ta taimaka matuka wajen bunkasar tattalin arzikin jama’ar Kasa, dubban jama’a ne suka samu abubuwan yi musamman ta fuskar kasuwanci.
“Kafin samar da wannan doka, daukacin kantunan Kwari suna hannun Inidiyawa da kwarori ne. Ita dai wanann kasuwa ta samo asali ne daga Kasuwar Kurmi, kasuwa mafi dadewa a tarihin arewacin sahara, a lokacin da kasuwar take a matsayin wurin da fatake ke zango a kan hanyarsu ta ratsa wanan lardi. Tun farko ana kiran Kasuwar Kantin Kwari da sunan ZANGON WAJE, masaukin bakin fatake masu shigowa Kano domin ciniki.
Alhaji Muhammad ya kara da cewa; “Zangon wajen ya kasance a unguwar Fagge ta Kudu, ya fara zama kasuwa ne sakamakon zuwan wasu larabawa daga garin Darma wanda ke kasar Libiya da kuma wasu Azbinawa daga Agadas. Wadannan ne suka fara ciniki a Kasuwar Kwari, wato Janbulo da ‘yan siminti, kuma sun fara wannan ciniki a lokacin Sarki Abbas a shekara ta 1903 zuwa 1919.
“A dai wanann lokaci ne Jirgin Kasa ya fara zuwa Kano har kuma aka samar masa da tasha kusa da zangon waje wanda yanzu ake kira Kasuwar Kwari. Wannan kasuwa taga juyi iri-iri, da farko kasuwar cinikin amfanin Gona ce saboda yawaitar noman rani da damina, kasancewar wurin cike yake da ruwa da Ni’imomi, wannan tasa fatake ke son sauka a wannan wuri saboda dausayinsa. Fatake na kaunar sauka a wurin tare da dabbobinsu, wannan ya faru a zamanin Kutumbawa a shekara ta 1623-1805, tun daga zamanin Sarki Abbas harkokin arziki suka fara bayyana a wannan wuri mai suna Zangon Waje, Kasuwar Kwari ta yanzu. A zamanin Sarkin Kano Usman Jirgin sama ya fara sauka a Kano a shekara 1919-1926 da wasu larabawan Siriya da suka zo Kano domin ciniki, kuma anan kasuwar Kantin kwari suka gudanar da harkokin kasuwancinsu. Haka kuma a zamanin mulkin Sarki Abdullahi Bayero wasu Kwarori suka zo Kano a shekara 1926-1953, suka zauna a sabuwar Kwari tun daga Gidan Amana har zuwa Kofar Fagge zuwa layin Jallaba.”