Bunkasar Nijeriya A Fagen Hulda Da Kasashen Ketare

Kasa Daya

Kalmar hulda da ke gudana a tsakanin kasa-da-kasa, wadda a Turance ake kira da Intanashinal Rileshin, “International Relations”, ta kunshin dukkan mu’amuloli ne da ke gudana a tsakanin Kasashen Duniya dake cin-gashin-kansu : huldar difilamasiyya, kasuwanci, yaki, wanzar da manufofin kasa da makamantansu, duka suna karkashin wannan kalma ta Intanashinal Rileshin, IT.

Za mu cigaba a mako mai zuwa

Mu’amala ta kasa da kasar, ta sami sharafi ne ainun, bayan kammala yakin Duniya na 2, musamman a nahiyar Amurka ta Arewa, hada da yankin nahiyar Turai ta yamma. Ta wata mahangar kuwa, a na la’akari da bunkasar mu’amular ne, bayan kammala yakin Cacar-baki a tsakanin manyan Kasashen Duniya, gawurtattun da ke da matsanancin karfin soji, irinsu Kasar Rasha da Amurka.

Kyakkyawar rawa abar yabo, da Nijeriya jiya ta taka a wannan fanni na mu’amulolin kasa da kasa, wani abu ne da wanda ke rayuwa a Nijeriya yau, zai kalla da tamkar mafarki ne ko almara. Babu shakka, wannan Kasa ta Nijeriya da muka tsinci kanmu cikinta, ta kasance wani katafaren yanki ne da Allah Yai masa baiwar komai da komai. Duk wata baiwa, ko wata falala, da kwakwalwa ka iya hakaita ko akasin haka, Allah Ya ba mu, kai-tsaye a Nijeriya, ko a kaikaice.

“…Giben its size, population, and bast natural resources endowment, Nigeria was perceibed at independence from colonial rule as a country destined to play crucial roles for progress and debelopment throughout the World and a natural leader on the African continent (Philips 1964 ; Thiam 1965).

Batun yin tsokaci bisa tsantsar baiwa da Allah Mahalicci Yai wa Kasata Nijeriya, ba zai zama wani kambame ba, duba da tarin rubuce-rubuce da manya masana a idon-duniya su ka labarta : wata jinjinar da kyawawan hasashe na ilmi da za a ji masanan na yi wa Nijeriya jiya, tamkar ma hankali ba shi iya dauka.

Wancan rubutu na Harshen Ingilishi da masana suka dubi Kasar Nijeriya jiya suka yi, a takaice, za a iya fassara shi ne kamar haka;

“… Duba da irin fadin Kasa, yawan bil’adama, da kuma mamakon albarkatun kasa da Nijeriya ke da, sai wadannan ni’imomi su ka sanya ake hasashen cewa, a duk sa’adda Nijeriya ta amshi mulki daga Turawan Mulkin Mallaka, to fa, Kasar, za ta taka muhimmiyar rawa, wajen kawo cigaba a Duniya bakidaya. Bugu da kari, Kasar ta Nijeriya, za ta zamto tamkar wata shugaba ta dindindin ga daukacin nahiyar Afurka…”.

Don Allah mai karatu, ka ji fa irin kallon da tun azal ake yi wa wannan Kasa tamu abar kaunarmu Nijeriya. Babu shakka, ganin irin rawar da Nijeriya jiyan ta fara takawa, a jiyan, ta fuskacin huldarta da Kasashen Duniya, sai zahiri ke nuna Kasar, ta dauko hanyar tabbatar da irin wadancan kyawawan hasashe ga Kasar a aikace.

 

Binkice ya tabbatar da cewa, Kasar Nijeriya, ta fara samun tagomashi ne a fagen hulda da Kasashen Duniya, a farko-farkon Shekarar da ta amshi mulki (1960) daga Turawan Birtaniya : lokacin da tsohon shugaban Amurka Lyndon B. Johnson ke gwama sunan Nijeriya da Algeria (Jega and Farris, 2010 : 3). Sai ya zamana, a duk sa’adda ya tasamma kira ko ambatar sunan Nijeriya, sai ya sha’afa ya ce Aljeriya.

 

A dai farko-farkon wancan lokaci na 1960, za a samu cewa, kusan Kasar Ingilishi ce kadai Kasar da Nijeriya ke yin mu’amalar kasuwanci da ita, inda Nijeriyar a farkon lamari ke fitar da kayan amfanin gona zuwa can Birtaniyar, har kawo lokacin da aka sanya cimma muradun karni gaba, za a ga cewa, Kasar Nijeriya, ta kasance guda daga manyan Kasashen Duniya, wadanda ke kan gaba wajen safarar albarkatun man fetur ga al’umar Duniya. Bugu da kari, Nijeriyar ce babbar mai safarar albarkatun man fetur din ga Kasar Amurka, sama da kowace Kasa a kudancin Saharar Afurka.

 

“…Nigeria has become an important player in international relations, an assumed potential leader of Africa, a major contributor to international peacekeeping and peacebuilding operations, both regionally and globally..” (Jega and Farris, 2010 : 3).

 

A wancan lokaci na Nijeriyar Jiya, lokacin da za a ce Kasar ta fi amsa sunanta sama da wannan lokaci da muke ciki ta fuskoki da dama, shi ne za ka ji Duniya ta kaure da yi wa Kasar tafi tare da jinjina, kamar yadda aka hakaito cikin wadancan sadarori da aka gabatar da su ta Harshen Turanci. Ga abinda ake cewa a takaice;

 

“…Babu shakka Kasar Nijeriya, ta kasance wata muhimmiya daga jerin masu ruwa da tsaki a huldodin kasa da kasa, ita ce kuma Kasar da ake wa kallo a matsayin jagorar Kasashen Afurka bakidaya. Bugu da kari, Kasar ta Nijeriya, na daga rukunin manyan Kasashen da ke ba da gagarumar gudunmuwa ga aiyukan kawo zaman lafiya gami da tabbatar da shi a nahiyar Afurka da sauran sasannin Duniya…”.

 

Mai karatu ya ji irin yadda Nijeriyar Jiya ta ke ko? Haka ma take a yau?. Ko da yake, da sauran tafiya, ya yi wuri, a fara bijirar da irin wadannan tambayoyi tun yanzu.

 

Wasu masana na da ra’ayin cewa, alakar kasa da kasa, ta fara bunkasa a wannan Kasa ta Nijeriya ne sa’adda aka kawo karshen yakin Cacar-baki da ya jima yana gudana a tsakanin wasu manyan Kasashen Duniya da ke da matsanancin karfin soja, musamman Kasar Amurka da Rasha. Daga wannan lokaci ne Nijeriyar Jiya, ta dauki azamar inganta alakarta ta kasa da kasa, tare da jan damarar taimakawa duk wani motsi ko kuduri game da samar da zaman lafiya a nahiyar Afurka da ma Duniya bakidaya, tare da jan damarar inganta tsarin Dimukradiyya a Duniya.

 

Exit mobile version