Connect with us

LABARAI

Buratai Bai Koma Katsina Ba – Rundunar Soji

Published

on

Rundunar Sojin kasar nan ta ce, babban hafsan dakarun kasa na kasar nan, Laftana Janar Tukur Buratai, ya je Katsina ziyarar aiki ce ta musamman domin ya gana da

rundunonin Sojin bataliya ta 8 da suke gudanar da ayyukan fatattakan ‘yan bindiga a can.
Rundunar Sojin ta ce ko kusa Buratai din bay a koma Katsina din ne ba a sakamakon karuwar hare-hare da kasha-kashen da ‘yan bindigar suke kaiwa a can din ba.
Hakanan ana sa ran Buratai zai halarci bukin ranar Sojoji ta wannan shekarar wanda ake sa ran farawa tun daga yau din nan har zuwa ranar 6 ga watan Yuli.
Bukin wanda da farko aka shirya gabatar da shi a Jos, ta Jihar Filato, sai aka mayar da shi garin na Kastina domin kara kwarin gwiwa ga dakarun Sojojin da suke aikin fafatawa da ‘yan bindigar a Jihar ta Katsina da sauran sassan arewa maso yammacin kasar nan.
Tun da farko Sojojin sun sanar da yin wani atisaye na musamman wanda aka sanya wa suna: Sahel Sanity, wanda a yanzun haka kuma ya fara haifar da da mai ido. Hakan kuma ba zai rasa nasaba da umurnin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bai wa Sojojin ba na gamawa da ‘yan bindigar da suka addabi mutanan Jihar da ma sauran sassan na arewa maso yammacin kasar nan ba.
Wannan fayyacewar da rundunar Sojin ta bayar ya zo ne domin musanta rahotannin da wasu ke bayarwa na cewa babban hafsan dakarun Sojin kasa na kasar nan ya tattara ya koma Katsina da zama har sai an ga bayan ‘yan ta’addan.
Mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar Sojin, Sagir Musa, y ace ziyarar ta Buratai za ta kara wa dakarun Sojin karfin gwiwa a kan aikin da suke yi na yakar ‘yan bindigar da sauran masu aikata laifuka a Jihar da sauran sassan arewa maso yammacin kasar nan.
Ya ce an fahimci maganar da babban hafsan ya yi ne a murgude a kan dalilin zuwan na shi Katsina.
Advertisement

labarai