Connect with us

JAKAR MAGORI

Buratai Ya Canja Sheka Zuwa Katsina

Published

on

A iya cewa a halin da ake ciki yanzu yaki da ‘yan bindiga ya sauya salo, yayin da shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai ya ce ya koma jihar Katsina.

A baya watanni kalilan da suka gabata, ‘yan bindiga sun saka jihar gaba inda suka gallabe al’umma da kai hare-hare. Buratai ya ce yana jihar ne don tsara yadda al’amuran sabbin atisayen da aka kaddamar su wanke jihar daga sharrin ‘yan bindiga. A ranar Litinin, 29 ga watan Yuni Shugaban rundunar sojin Nijeriyar, Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, ya sanar da komawarsa kacokan zuwa jihar Katsina bayan tsanantar hare-haren ‘yan bindiga a jihar. Buratai ya sauka a jihar ne don tsara yadda al’amuran sabon atisayen da suka kaddamar, wanda aka shirya su don kakkabe ‘yan bindiga daga yankin Arewa maso Yamma zai kasance.

“Na iso ne tun kwanaki biyu da suka gabata kuma zan kwashi wani lokaci don shirya ayyukan dakarunmu da kuma yadda za mu shawo kan wasu kalubale da suka addabe mu,” Buratai ya sanar da gwamna Aminu Masari bayan ziyarar da ya kai masa. Ya kara da cewa: “Mun san yadda tsaron yankin Arewa maso Yamma ya tagayyara, wanda a halin yanzu ya zama abIn daga hankali. “Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin fitar da tsari ko matakai masu kyau daga cibiyoyin tsaro.

“Daga cikin kokarinmu na ganin mun bi umarnin shugaban kasa na samar da tsaro mai daidaituwa, rundunar sojin Nijeriya ta hada ayyukanta da sauran cibiyoyin tsaro a nan yankin Arewa maso Yamma.”

A martanin Gwamna Aminu Masari, ya jajanta yadda ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a sassan jihar. Hakan ya sa wasu sassan jihar aka kasa shugabantarsu. Kamar yadda gwamnan ya ce, jihar tana fuskanci miyagun ayyukan ‘yan bindigar wanda hakan ya sa jama’a ke tserewa gudun hijira. in ji shi “Abin da mutanen nan suka sani shi ne karfi kuma har sai mun fi karfinsu sannan ne za mu iya shawo kan matasalar da ta addabe mu. “A don haka ina kira ga cibiyoyin tsaro da su gane cewa ‘yan bindigar nan ba su fahimtar wani yari da ya wuce ruwan wuta.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: