Babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai a ranar Talata ya ziyarci Asibitin Sojojin Nijeriya 44, Kaduna, inda ya duba sojojin da suka samu raunuka dake karkashin rundunar OPERATION LAFIYA DOLE da SAHEL SANITY.
Ya kuma duba wasu ayyukan da ke gudana tare da kaddamar da ayyukan da aka kammala a Co barracks.
A ranar Litinin din da ta gabata ne Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji ya ziyarci sojojin da suka jikkata inda wani memba a kwamitin, Sanata Sulieman Abdulkadir ya yi kira ga gwamnonin jihohi da su sake bai wa jaruman sojojin wata dama acikin wasu ayyukan gwamanti ta hanyar samar musu da ayyukan yi.
Ya kara da cewa “COAS ya zo ne musamman don duba marasa lafiya na Operation Lafiya Dole da Operation Sahel Sanity a asibiti,”
Wata majiya tace kimanin sojoji 416 da suka samu raunuka a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya a jihar Borno a yanzu haka suna kwance ne a asibitin 44 na Sojojin Nijeriya, Kaduna.