Wannan hira ce da wakilimmu, IBRAHIM MUHAMMAD Kano ya yi da shugaban Karamar Hukumar Bagwai ta jihar Kano, HON. INUWA ZANGINA RIMIN GADA, inda ya tabo kadan daga nasarorinsa da ya samu a dan takaitaccen lokacin da bai wuce watanni ba da zama shugaban Karanar Hukumar. Wanda yanzu haka al’ummar yankin sun sake ba shi dama ta sake yin takara shugabancin a zabe mai zuwa. Ga yadda tattaunawar tasu ta kasance.
Mun san lokacin da ka karbi ragamar mulkin nan, bayan tsohon shugaban , Hon. Yusuf Badai ya zama dan Majalisar tarayya, kai ne ka dora akan irin abubuwa da kuka somo, yanzu gashi kuna daf da karasa karshen zangon mulki. Me ka dora a kai daga kama shugabancin, wanda ya ke faranta maka rai da shi tun daga zama shugaban Bagwai?
Ni yanzu ban fi watanni Takwas zuwa 10 da zama shugaban Karamar Hukuma ba, domin an rantsar da ni a watan Biyu na wannan Shekarar ranar 26 ga wata.To Allah ya sani mun yi iya kokarimmu domin mu dora al’umma a layi mai kyau. Mun yi iya kokarinmu don mutane su amfana. Misali, inka dubi daga lokacin da na karbi shugabancin bagwai zuwa yanzu, na yi katafaren ginin wata babbar gada da ke Yalawai kafin a shiga Bagwai, na yi ta wanda a baya karyewa ta yi.
Bayan nan, a wannna lokacin na sami dama na dauki mutane 25 aiki na dindindin wanda shim a abu ne da dan’adam zai yi alfahari da shi, domin sama wa mutum aiki ba karamin abu ba ne. Bayan nan, akwai wani aiki da ke da mutukar muhimmanci da yake ci wa al’ummar Bagwai tuwo a kwarya, akwai gyaran wutar lantarki akalla a mazaba hudu, daga Bagwai ya yi Yamma har zuwa karshen Bagwai, mazabun Wurobagga, Gogori, Sarisare da Gadanya, su ma sun shafe kusan shekaru Goma sha babu wutar lantarki, amma yanzu gashi na yi kokari na gyara musu, yanzu in ka je za ka samu suna da wutar lantarki.
Akwai wasu ayyuka da na shiga na fita a ma’aikatar ruwa aka zo aka haka rijiyoyi masu aiki da hasken rana aka sa masu tanki guda Bakwai a Karamar Hukumar Bagwai, wanda shi ma na ke jin dadi a lokacina aka yi shi.
Bayan nan, wajen gudanar da aikin ofis, na zo ni na sayi motar shugaban Karamar Hukuma kasancewar wancan na da matsaloli, da na Sakataren ilimi na Karamar Hukuma. Haka motar Hakimi da ta yi hatsari, na saya masa wata, haka an saiwa Sakataren mulki na Karamar Hukuma mota sakamakon tasa ta tsufa, da abubuwa dai da yawa. Akwai shugaban Kansiloli ma ni na saya masa mota. kuma akwai shiri ma na saya wa hukumomin tsaro da ke yankin motocin aiki. Allah ya sani dan lokacin da na samu ina matukar alfahari da wadannan abubuwan.
Za a iya cewa Bagwai yanki ne da ke da dimbin manoma na rani da damina da take bada gudummuwa wajen ciyar da al’umma. A zuwanka akwai wani yunkuri ne da ka yi a wannan bangare?
To da yake ban dade ba, kuma ban taba bangaren noma ba, kuma dama su al’ummar Bagwai noma suke kokarin yi da kansu, ba tare da dogaro da Gwamnati ba, suna na rani da na damina ba tare da jira sai Gwamnati ta yi abu kaza ta yi abu kaza ba. Amma cikin ikon Allah yanzu da muke sa ran Allah zai sake ara mana wani lokacin in Allah ya yarda za mu tsaya mu kalli irin gudumnuwa da za mu bayar akan harkar noma, da yardar Allah.
Ganin cewa a ‘yan watanni da ka yi ka gudanar da ayyuka da dama, wane irin matakai ka bi dan cimma wadannan nasarorin?
To muhimman abu dai shi ne kwantar da hankali da biyayya da ganin girman nagaba. Ba abin da harkar nan illa ka yi biyayya, wannan ta sa tsakanina da Kwamishirnan Kananan Hukumomi akwai zaman lafiya, akwai biyayya tsakanina da mai girma Gwamna da dukkan shugabanni namu, muna girmama su, duk wanda ka ke girmamawa in ka tura bukatarka sai ya ba ka dama da goyon bayan cimma nasara.
Zababbun Kansiloli da ma’aikata su ne ake tafiya da su domin cimma nasara, yaya dangantakarku ta ke kasancewa?
Yaya zaman lafiya a tsakanin al’umnar karanar hukumar Bagwai?
Al’ummar Bagwai dama masu son zaman lafiya da kwanciyar hankali ne, domin duk inda ka ga ana tashin hankali, akwai matsala ta talauci da shaye-shaye. Mu al’ummar Bagwai manoma ne kuma ‘yan kasuwa ne, ina tabbatar maka duk wanda ka gani burinsa in gari ya waye ya ta fi gona ko kasuwa ko wajen aiki, shi ya sa ake zaune lafiya da kowa da kowa, ba mu da wata matsala.
Al’umma a Bagwai sun nemi ka dawo, zuwa yanzu ko ka amsa wannan kiran?
Ni dai ina tabbatar maka ma, zuwa yanzu ni ne dan takarar jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Bagwai, kuma ina da kyakkyawan sa rai, ni ne zan yi nasarar komawa shugabacin. Ina tabbatar maka da cewa kamar yadda muka faro aiki na alheri, da mun zo kawai dorawa za mu yi akai da yardar Allah.
Mene ne kiranka ga al’ummar Bagwai ?
Kirana ga al’ummar Karamar hHukumar Bagwai shi ne, duk lokacin da aka ce wane shugaba ne, jagora ne, to babban abu shi ne a rika taya shi da addu’a, idan aka ce an kyale mutum ana kallon shi yake da wayo ko yake da iyawa, to iyawarsa ba za ta wadatar da shi ba. Amma in aka zo a duk inda jama’a ke taruwa, masallatai da makarantu da wurare na cin abinci, ko wurin mai shayi, a rika kyakkyawan zaton cewa wane ya zo da niyyar yi mana abin kirki, mu rika taya shi da addu’a, cikin yardar Allah sai ka ga ya dawo da hankalinsa, inda zai rika ayyuka na alheri.